Kun Iya Sanya ‘Uniform’ Kuna Yawo, Amma Kun Gaza Tsayar da Dan Takara Daya, Shehu Sani Ga ’Yan G5
- Shehu Sani, tsohon sanata kuma dan gwagwarmaya a Kaduna ya yi martani kan rabuwar kan gwamnonin G5
- Sanatan ya ce tafi shafinsa na Twitter, inda ya zolayi gwamna Nyesom Wike na Ribas da tarin abokan tafiyarsa
- A cewar Shehu Sani, gwamnonin G5 da suka dama PDP sun saba ra’ayi bayan shafe watanni bakwai suna yawo a kasashen duniya tare da kin dan takarar jam’iyyarsu
Jihar Kaduna - Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya yiwa gwamnonin PDP na G5 zolayar rashin hadin kai da suka samu kwanan nan.
A wani rubutun da ya yada a Twitter a ranar 22 ga watan Faburairu, dan siyasan kuma dan gwagwarmaya ya ce, gamayyar G5 ta raba gari duk da kuwa da yadda ta kullaci dan takarar shugaban kasa na PDP a baya.
Shehu Sani yace, abin mamaki ne hakan, ganin yadda suke yawo kasa-kasa don ganawa da yin kus-kus a adawarsu da Atiku da shugabancin PDP.
Zolayar Shehu Sani kan gwamnonin G5
A rubutun da ya yi Twitter a ranar Laraba, Shehu Sani ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Gwamnonin G5 sun sanya kaya iri daya na tsawon watanni bakwai a Landan, Madrid da Paris amma sun gaza tsayar da dan takara iri daya.”
Idan baku manta ba, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP ya fuskanci kalubale da kiyayya daga gwamnonin jihohi biyar kuma na PDP saboda wasu dalilai.
Daga cikin abin da gwamnonin ke nuni dashi shine, basu amince shugaban PDP na yanzu, Ayu Iyorchia ya ci gaba da rike shugabancin jam’iyyar ba.
Ya zuwa yanzu dai ba a daidaita da dan takarar shugaban kasan da gwamnonin 5 ba, ga kuma zaben 2023 na kara karatowa, saura kwanaki kasa da uku.
Yadda Atiku ya caccaki gwamna Wike kan alakarsa da Tinubu
A wani labarin na daban, kunji yadda dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ya caccaki gwamna Wike na jihar Ribas.
A cewar Atiku, Wike ba zai iya tabbatar da samawa dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu kuri’un jihar Ribas ba a zaben bana.
Saura kwanaki kadan a yi zaben shugaban kasa a Najeriya, har yanzu akwai bunu a kaban jam’iyyar PDP.
Asali: Legit.ng