CBN Ya Fara Rabawa Mutane Takardun Sabon Naira Gida-Gida a Kano

CBN Ya Fara Rabawa Mutane Takardun Sabon Naira Gida-Gida a Kano

  • Babban bankin Najeriya (CBN) ya fara shirin zuwa gida-gida musanya wa mutane sabbin takardun naira
  • Hakan na zuwa ne yayin da ake tsaka da wahalhalun rashin isassun kuɗin, lamarin da ya jefa yan Najeriya da yawa cikin kunci
  • CBN na fatan wannan sabon yunkurin zai taimaka wajen rage ƙuncin karancin sabbin naira da kuma rage raɗaɗi ga al'umma

Abuja - Babban bankin Najeriya (CBN) ya kara ɗaukar matakin zuwa gida-gida domin musanya wa mutane sabbin naira a jihar Kano.

CBN ya tura wakilai zuwa kananan hukumomi uku a Kano, sun ƙunshi Rano, Kibiya da Tudun Wada.

Sabbin naira.
CBN Ya Fara Rabawa Mutane Takardun Sabon Naira Gida-Gida a Kano Hoto: CBN
Asali: Twitter

Wakilan babban bankin sun shaida wa yan jarida cewa an kirkiro wannan shirin ne da nufin rage kuncin rashin isassun naira a jihar da kuma baiwa mutane damar musanya tsohon kuɗinsu da sabbi cikin sauki.

Kara karanta wannan

An Samu Ci Gaba: CBN Ya Ɗauki Mataki Mai Kyau Yayin da Yan Najeriya Ke Kai Tsoffi Naira Bankuna

Ɗaya daga cikin wakilan CBN ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"CBN ya gama duk wasu shirye-shiryen raba sabbin kuɗi zuwa ƙauyuka, wuraren da babu Tituna masu kyau ko rassan bankuna, ta haka ne kaɗai zasu amfana da musanya tsoffin kuɗinsu da sabbi."

Jaridar Bussiness Day ta rahoto cewa CBN ya sha alwashin ƙara faɗaɗa wannan shiri na zuwa gida-gida musanya kuɗin a sauran ƙananan hukumomin jihar Kano.

Kanawa sun samu sauki

Ana tsammanin matakin da CBN ya dauka na raba sabbin naira ga mazauna jihar Kano zai rage masu radadin kuncin rayuwan da suke fama da shi da wahalar neman tsabar kuɗi.

Lamarin karancin kuɗin ya taba rayuwar mutane ta yau da kullum, inda 'yan Najeriya da dama suka shiga damuwa sakamakom rashin iya sayen kayan abinci da kuma tafiye-tafiye.

Kara karanta wannan

Waraka Ta Samu: CBN Ya Ɗauki Sabbin Matakai Masu Kyau, Ya Sake Fito da Tsoffin Naira N200

Mutane Sun Ci Gaba da Kai Tsohon Naira Bankuna Yayin da CBN Ya Bar Shafi a Bude

A wani labarin kun ji cewa CBN ya bar Fotal ɗin maida tsoffin kuɗi a bude duk da wa'adin 17 ga wata ya cika, kwastomomi sun yi amfani da wannan dama.

Bayanai sun nuna cewa har zuwa ranar Litinin shafin maida tsoffin naira na CBN na bude, lamarin da mutane suka yaba duba da halin da ake ciki.

Sai dai wasu kwastomomi sun nuna damuwarsu kan yadda ko sun bi matakan da aka tsara sun kai tsoffin kuɗin, ba su ganin Alat a Asusun banki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel