Sarki Ya Bijire Wa Umurnin Buhari Da CBN, Ya Ce Al'ummarsa Su Cigaba Da Hada-Hada Da Tsaffin Kudi

Sarki Ya Bijire Wa Umurnin Buhari Da CBN, Ya Ce Al'ummarsa Su Cigaba Da Hada-Hada Da Tsaffin Kudi

  • Wani basaraken gargajiya ya umarci al'ummar garin sa da su cigaba da karbar tsohon kudi bayan sun kona bankuna biyu a zanga-zanga
  • Sarkin Akarigbo na kasar Remo ya dauki alkawarin babu wanda zai yi asarar tsohon kudi idan ya karba daga wajen abokan huldar sa
  • An shafe sama da sati biyu ana gudanar da zanga-zanga a sassa daban daban saboda karancin takardun kudi

Jihar Ogun - Akarigbo na kasar Remo, Babatunde Ajayi, ya roki mutane a yankin sa da su cigaba da karbar tsohon kudi, bayan masu zanga-zanga ranar Litinin sun kona bankuna biyu a kusa da fadarsa a Sagamu.

Zanga-zangar ta taso ne sanadiyar wahalar rashin sababbin kudi da kuma hauhawar farashin man fetur, Premium Times ta rahoto.

Zanga-zanga
Sarki Ya Fada Wa Al'ummarsa Su Cigaba Da Hada-Hada Da Tsaffin Kudi Bayan Mummunan Zanga-Zanga. Hoto: Leadership
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Hadimar Aisha Buhari ta tafi kotu, ta ce matar Buhari ta ci zarafinta, a bata diyyar N100m

Masu zanga-zangar sun fara da kona tayoyi kafin daga bisani su kona bankunan, lamarin da ya jefa garin cikin hargitsi.

Bankunan da aka kona ba su fi tafiyar mita 300 daga fadar basaraken ba.

An fara zanga-zangar ta hanyar lumana daga gaban fadar amma daga baya rikici ya barke bayan jami'an tsaro sun isa wajen.

A wata sanarwa bayan zanga-zangar, basaraken ya ce:

''Ina rokon kowa ya kwantar da hankalinsa saboda muna ta kokarin tattauna wa da gwamnatin tarayya.
''Wannan tsarin ba daga jiha ko karamar hukuma ba ne. Saboda haka, barnatar da dukiya da rayuka ba abin da zai haifar sai kara ta'azzara lamarin.
''Ina rokon mutanen mu da su cigaba da karbar tsohon kudi saboda umarnin kotun koli. Ba wanda zai yi asarar tsohon kudi idan ya karba. Zan iya baku tabbacin haka, kuma ina rokon ku da ko rike wannan alkawarin.''
''Sannan, ina umartar duk yan kasuwa da su cigaba da karbar tsohon kudi. Na daukar mu ku alkawarin cewa ba wanda zai yi asarar tsofaffin kudin da ya ke da su.''

Kara karanta wannan

Karancin Kudi: Gwamna Ya Samar Da Bas Din Kyauta Don Ragewa Al'ummarsa Radadin Halin Da Ake Ciki

Ana cigaba da zanga-zanga musamman a Abeokuta, babban birnin jihar, na kusan tsahon sati biyu sabo da rashin kudin.

Gwamnan Ogun ya yi barazanar rufe duk bankuna da ba su karbar tsaffin kudi

Tun da farko kun ji cewa Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya yi wa bankunan kasuwanci da ba su karbar tsaffin takardun naira barazana cewa zai rufe su.

Gwamna Abiodun ya yi wannan barazanar ne yayin da ya ke jawabi ga mutane yan kasuwa da ke Itoku Kampala a ranar Talata da ta gabata yana mai cewa gwamnatinsa na aiki don warware matsalar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel