Gwamnatin Kogi Ta Tabbatar da Tashin Bam a Karamar Hukumar Okehi
- Gwamnatin jihar Kogi da ke arewa ta tsakiya ta tabbatar da tashin Bam a Sakatariyar ƙaramar hukumar Okehi
- Mai baiwa gwamna shawara kan harkokin tsaro, Mista Omodara, ya ce ba'a rasa rai ko guda ba, ya faɗi manufar masu hannu
- Rahotanni sun bayyana cewa wasu yan bindiga ne suka kai hari Sakatariyar ranar Litinin da daddare
Kogi - Gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da tashin wani abun fashewa da ake kyautata zaton Bam ne a Sakatariyar ƙaramar hukumar Okehi ranar Litinin da daddare.
Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na jihar, Duro Jerry Omodara, ne ya tabbatar da tashin bam ɗin a Lokoja, babban birnin jihar ranar Talata.
Ya ce lamarin yana da alaƙa da masu yunkurin ta da yamutsi a lokacin zaɓe domin hana mutane su fito cikin kwanciyar hankali su kaɗa ƙuri'unsu.
Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Gamu da Gamonsu, An Kashe Su Baki Ɗaya Yayin da Sukai Yunkurin Kai Hari
Mista Omodara ya bayyana cewa babu ko mutun ɗaya da ya mutu sanadin lamarin kuma a halin yanzun jami'an tsaro sun kewaye yankin domin dawo da komai daidai.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Me ya faru tun farko?
Vanguard ta tattaro cewa wasu 'yan bindiga da ba'a gano ba har yau ne suka kutsa cikin Sakatariyar kana suka tashi ofishin shugabanci.
Wannan harin na zuwa ne yayin da ya rage kwanaki 5 kacal babban zaɓen shugaban kasa wanda zai gudana ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023, a cewar rahoton Daily Post.
Kusan watanni biyu da suka gabata, makamancin irin haka ta faru a wannan yankin mazaɓar Sanatan, inda wani bam ya tashi a fadar Basaraken ƙasar Ebira.
Lamarin ya faru ne yayin da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya kai ziyara jihar, inda ya kaddamar da wasu ayyukan raya kasa da gwamna Yahaya Bello ya kammala.
'Yan Ta'adda Sun Cinna Wa Dattijuwa Wuta Da Ranta Ta Ƙone Ƙurmus
A wani labarin kuma Yan bindiga sun halaka wata tsohuwa yayin da suka bankawa gidaje wuta a jihar Imo
Rahotanni sun tabbatar da cewa matar mai shekaru da yawa ta ƙone kurmus lokacin da yan ta'addan suka banka wa gidaje wuta a garin Amagu Ihube, karamar hukumar Okigwe ranar Talata.
An tattaro cewa daga cikin gidajen da harin ya shafa har da na kwamishinan matasa da wasanni na jihar Imo, Emeka Okoronkwo.
Asali: Legit.ng