'Yan Sanda Sun Gurfanar da Wani Matashin da Ya Yi Barazanar Kashe Mahaifinsa a Benue

'Yan Sanda Sun Gurfanar da Wani Matashin da Ya Yi Barazanar Kashe Mahaifinsa a Benue

  • An gurfanar da wani matashin da ya yi barazanar kashe mahaifinsa idan bai bashi wani adadin kudi ba
  • Moses Eche ya musanta zargin da ake masa, ya ce shi sam bai yiwa mahaifinsa barazanar komai ba
  • An dage ci gaba da sauraran kara zuwa ranar 21 ga watan Maris don sake jin hujjoji da bayanan bincike

Jihar Benue - ‘Yan sanda a jihar Benue sun yi nasarar kame wani mutum mai suna Moses Eche mai shekaru 37 a birnin Makurdi ranar Litinin bisa zarginsa da kokarin aikata mummunan aikin ta’aaddanci.

Hakazalika, an gurfanar da matashin a gaban kotun don amsa laifin da ake zarginsa dashi, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Jami’ar ‘yar sanda mai gabatar da kara, Insp. Rachael Mchiave ta shaidawa kotun cewa, wanda ka zargin a ranar 16 ga watan Faburairun 2023 ya yi barazanar hallaka mataifinsa mai suna Daniel Eche idan bai bashi wasu adadi na kudi ba.

Kara karanta wannan

An Kama Dan Sanda Da Ya Bindige Dattijuwa Yar Shekara 80 Har Lahira A Adamawa

Yadda matashi ya yi barazanar kashe mahaifinsa a Benue
'Yan Sanda Sun Gurfanar da Wani Matashin da Ya Yi Barazanar Kashe Mahaifinsa a Benue | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ta kara da cewa, laifin da matashin ya aikata ya saba da kudin dokar jihar Benue, 2004, rahoton kafar labaran tsegumi ta LindaIkeji.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarta, ana ci gaba da bincike kan lamarin kuma nan ba da jimawa ba za a gabatar da cikakkun bayanai a gaban kotu.

Ban aikata komai ba, inji wanda ake zargi

Sai dai, da aka karanto masa laifin da ya aikata, matashin ya musanta dukkan abubuwan da ake tuhumarsa da aikatawa.

Ya zuwa yanzu, mai shari’a a kotun majistare da aka gurfanar da matashin, Mrs. Dooshima Ikpambses ta ba da belin matashin kan N50,000 tare da kawo masu tsaya masa.

Hakazalika, an dage ci gaba da sauraran karar har zuwa ranar 21 ga watan Maris din bana idan Allah ya kaimu.

Matashi ya biya kudi don a kashe mahaifinsa a jihar Neja

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Matashi Dan Shekara 20 Ya Yi Garkuwa Da Mahaifiyarsa A Zamfara, Ya Karbi Miliyan 30 Kudin Fansa

A wani labarin kuma, an kama wani matashi a jihar yayin da ya ba da makudan kudade domin wani abokinsa ya hallaka mahaifinsa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace matashin ya ba da kudi N110,000 domin kawai a kai mahaifinsa rami ba tare da wani kwakkwaran dalili ba.

Rundunar ta bayyana cewa, matashin ya yi hakan ne domin kawai ya samu damar cin gadon mahaifin nasa, kuma an kashe dattijon, an tsinci gawarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.