Sauki Ya Samu: Babban Banki CBN Ya Sake Fito da Tsoffin Takardun N200

Sauki Ya Samu: Babban Banki CBN Ya Sake Fito da Tsoffin Takardun N200

  • CBN ya bayyana cewa nan da yan kwanaki mutane zasu wadata da tsoffi da sabbin takardun naira N200
  • A makon da ya shige ne shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya umarci CBN ya sakarwa mutane tsoffin N200
  • Wasu ma'aikata a babban bankin sun bayyana shirin da ke a ƙasa wanda 'yan Najeriya zasu ji daɗinsa

Abuja - Babban bankin Najeriya (CBN) ya tabbatar da cewa ya sake fito da tsohon takardun N200 kuma ya raba wa Bankuna domin yan Najeriya su samu ikon ci gaba da hada-hada da su.

Amma rahoton The Nation ya bayyana cewa babban bankin ya yi gum da bakinsa kan adadin yawan takardun N200 da ya sake turo wa zuwa hannun jama'a.

Takardun N200.
Sauki Ya Samu: Babban Banki CBN Ya Sake Fito da Tsoffin Takardun N200 Hoto: thenation
Asali: UGC

Mafi yawan takardun N200 da CBN ke ikirarin ya sako tsofaffi ne da aka taɓa amfani da su kuma da yawansu an karɓe su daga hannun yan Najeriya lokacin shirin musayar kuɗi.

Kara karanta wannan

"Kana Jawo Kama Tashin Hankali" Gwamna Wike Ya Ɗau Zafi, Ya Aike da Sako Ga Buhari da Atiku Kan Sabbin Naira

Wani ma'aikacin CBN ya shaida wa jaridar cewa adadin takardun naira N200 da ke yawo a hannun al'umma ya ƙaru bayan umarnin da shugaban kasa ya bayar a makon da ya shige.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mutumin, wanda ya ƙi faɗin sunansa saboda ba shi da hurumin magana kan lamarin, ya ce, "Sun raba tsoffin da sabbin N200 a ƙarshen makon nan."

Ya ce rassan CBN a jihohin Najeriya, "Sun karbi takardun naira a ƙarshen makon nan kuma zuwa ranar Litinin da safe zasu fara rabawa bankunan kasuwanci."

Haka zalika ya jaddada cewa bankuna sun karbi isassun takrdun N200 da zasu zuba a na'urar ATM domin su isa hannun mutane.

Sai dai ya ƙi ya bayyana dadin yawan takardun kuɗin da suka baiwa bankuna domin ta haka ne kaɗai za'a iya gane tasirin da zasu yi wajen rage raɗaɗin halin da mutane ke ciki.

Kara karanta wannan

"Ka Bani Mamaki" Gwamna Wike Ya Maida Martani Ga Jawabin Shugaba Buhari Kan Karancin Naira

Wani ma'aikacin CBN na daban kuma ya faɗa wa The Nation cewa:

"Adadin yawan takardun N200 sun ƙaru sosai a hannun jama'a fiye da makon da ya gabata."

A cewarsa, mutane zasu fara ganin sabbi da tsofaffin N200 nan da yan kwanaki kaɗan saboda tuni CBN ya cika bankuna da takardun naira kuma ana tsammanin zasu baiwa yan Najeriya.

Adamu, El-Rufai da Wasu Gwamnoni 3 Sun Gana da Malami Kan Canja Naira

A wani labarin kuma Shugaban APC da wasu gwamnoni huɗu sun gana da Ministan Shari'a a birnin tarayya Abuja

Gwamna Malam Nasiru El-Rufai na Kaduna na ɗaya daga cikin gwamnonin da suka halarci ganawar ranar Litinin 20 ga watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262