Atiku Ne Dan Takarar Shugaban Kasa Na Arewa, Inji Jigon Kungiyar ’Yan Arewa Ta ACF
- Zauren tuntuba na Arewa (ACF) ya bayyana cewa, Atiku Abubakar ne dan takarar shugaban kasa na shiyyar Arewa
- Jigon kungiyar ne ya fito ya yi bayani, inda yace Atiku za a zaba a zaben 2023 mai zuwa nan ba da jimawa ba
- Saura kwanaki kadan zabe, 'yan Najeriya na ci gaba da fuskantar kalubale tare da dasa ayoyin tambayoyi game da zaben bana
Jihar Sokoto - Jigon zauren tuntuba na Arewa (ACF), Muhammad Yakubu ya ce, Atiku Abubakar ne dan takarar shugaban kasan da kungiyar za ta ta goya wa baya a zaben bana.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, ACF ta fitar da sanarwar da ke shawartar ‘yan Najeriya da su zabi dan takarar da suka ga ya dace a tunaninsu.
Wannan sanarwa ta ACF ta fto ne daga hannun babban sakatarenta, Murtala Aliu a ranar Lahadi 19 ga watan Faburairu.
ACF ta bukaci ‘yan Arewa da su yi duga ga dan takarar shugaban kasan da ke manufofi masu kyau kuma mutum mai dabi’a don ba shi kuri’unsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ne dan takarar da ‘yan Arewa za su zaba, inji jigon ACF
Sai dai, a wannan karon da yake jawabi a wani taron manema labarai a Sokoto a ranar Litinin 20 Faburairu, 2023, Yakubu, wanda shine mataimakin oditan kungiyar ya ce sun zabi Atiku.
A cewarsa, bayanan da suka fito daga jiga-jigan kungiyar kamar su Alhaji Zango Daura, Farfesa Ango Abdullahi da sauransu duk sun bayyana Atiku za a kada wa kuri’a.
Jigon na ACF ya kasance daya daga cikin masu tallata tafiyar Atiku da Okowa a cikin wata kungiyar mai suna Atiku/okowa Patriots.
Ya ce, sun zabi Atiku ne ba don kasancewarsa dan Arewa ba, sai don duba da kwarewa, gogewa da kuma manufofinsa na gari da suka hango, Tribune Online ta tattaro.
Limaman Katolika sun ce a zabi mai gaskiya da rikon amana
A wani labarin kuma, Limaman cocin Katolika sun bayyana gukatar a zabi wanda ya cancanta ya gej kujerar Buhari a zaben bana.
Limaman sun ce, ya kamata 'yan Najeriya su farga su fahimci yanayin da ake ciki su zabi wanda zai share musu kuka.
Hakazalika, sun yi kira ga Buhari da CBN da su kawo karshen yananyin wahala da kasar ke ciki.
Asali: Legit.ng