Tashin Hankali Yayin da Aka Harbe Wani Mamban Jam’iyyar APC a Taron Gangamin Osun

Tashin Hankali Yayin da Aka Harbe Wani Mamban Jam’iyyar APC a Taron Gangamin Osun

  • Jam'iyyar APC a jihar Osun ta yi rashin wani mambanta yayin da aka kai farmaki a lokacin kamfen na karamar hukumar Ilesa
  • An hallaka mamban ne tare da zargin wasu tsagerun 'yan daban jam'iyyar PDP da aikata wannan mummunan aikin
  • A bangare guda, PDP ta ce ba gaskiya bane, kuma ta zargi APC da farmakar wasu jiga-jiganta a jihar

Jihar Osun - Wani mamban jam'iyyar APC, Ebenezer Alaro ya kwanta dama yayin da aka bindige shi a taron gangamin kamfen din jam'iyyar a karamar hukumar Ilesa ta jihar Osun.

Jaridar The Nation ta tattaro cewa, Alaro wanda daya ne daga jiga-jigan taron gangamin an harbe shi ne a unguwar Irojo da ke Ilesa.

Wannnan batu na fitowa ne daga wata sanarwar da shugaban jam'iyyar APC, Tajuddeen Lawal, inda ya zargi wasu tsagerun PDP da aikata wannan barna.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Hadu Da Gagarumin Cikas a Arewa: Dan Takarar Gwamnan LP a Kano Ya Yi Maja a APC

An hallaka jigon APC a wurin kamfen a Osun
Tashin Hankali Yayin da Aka Harbe Wani Mamban Jam’iyyar APC a Taron Gangamin Osun | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Dan takarar PDP ne ya dauki nauyin harin

Ya kuma bayyana zargin cewa, dan takarar majalisar wakilai na Ijesa-South, Sanya Omirin ne ya dauki nauyin wannan ta'addanci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya shaida cewa, tsagerun 'yan daban da suka aikata aikin sun yi shiga ne irin na 'yan sanda a lokacin da ake gudanar da taron.

Lawal ya siffanta kisan da abin ki kuma aiki na ta'addanci da bai kamata a yiwa wani dan jam'iyyar ba, rahoton Punch.

A cewarsa:

"Abin tausayi ne yadda jam'iyyar PDP mai mulkin jihar ta dauki tashin hankali a matsayin hanyar nasara ga jam'iyyar a babban zabe mai zuwa."

Duk makircin APC ne, PDP ta magantu

Sai dai, mukaddashin jam'iyyar PDP na jihar, Dr. Akindele Adekunle ya zargi tsagerun 'yan daban APC da kai hari gidan Omirin, inda suka kusan kashe mahaifinsa tsoho tukuf.

Kara karanta wannan

An Kama Dan Sanda Da Ya Bindige Dattijuwa Yar Shekara 80 Har Lahira A Adamawa

Ya zargi cewa, an kai farmaki gidan tsohon shugaban jam'iyyar, Sunday Bisi duk dai a irin wannan yanayi.

Hakazalika, ya ce wannan farmaki na APC ba komai bane face kokarin sanya tsoro a zukatan 'yan PDP tare da hana su zuwa filin zabe.

Wannan lamari dai na zuwa ne bayan da aka kashe wani dan babban jigon jam'iyyar APC a jihar Legas da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.