Ganduje ya shirya yaki, ya fadi yadda zai hukunta bankin da bai karbar N500, N1000
- Dr. Abdullahi Umar Ganduje zai kafar wando daya da bankunan da ke kin karbar tsofaffin kudi
- Gwamnan Jihar Kano ya ce kin amincewa da tsofaffin N500 da N1000 zai jawowa mutane asara
- Ganduje yace zai rushe bankin da ya ki karbar tsohon kudi, sai ya gina makaranta a madadinsa
Kano - Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya gargadi masu harkar kasuwancin banki a jihar Kano da ba su yarda su karbi tsofaffin kudin da aka canza.
Channels TV ta rahoto Dr. Abdullahi Umar Ganduje yana barazanar rusa bankunan da ba su amincewa su yi kasuwanci da tsofaffin N500 da N1000.
Mai girma Gwamnan ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake duba kayan abincin da za a rabawa al’umma saboda radadin rayuwar da ake fama da shi.
Da yake bayani a ranar Juma’ar da ta gabata, Gwamnan ya ce ba zai amince bankuna su rika yi wa umarnin kotun karon tsaye a kan batun canjin kudi ba.
CBN zai jawowa mutane asara
Gidan rediyon Express Radio Nigeria ya rahoto Gwamna Abdullahi Ganduje ya ce Najeriya ba mallakin gwamnan babban banki, Godwin Emefiele ba ce.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan yake cewa duk bankin da bai amfani da kudin da aka sauya, zai jawo al’umma su yi asara kenan, ya nuna ba za su yarda da haka a Kano ba.
Dr. Ganduje ya kafa kwamiti da zai sa ido, kuma ya bukaci mutane su kawo karar bankin da ya saba domin a karbe masa lasisi, sannan a ruguza gininsu.
Abin da Gwamna ya fadawa jama'a
Inda ake cinikayya, a cigaba da amfani da tsofaffin kudi, domin sababbin kudin ma babu su, saboda haka muna rokonku, ku cigaba.
Kuma duk bankin da ya ki karbar tsofaffin kudi watau mutane suyi asara kenan, a kawo mana sunan wannan bankin.
Dama kuma mun sa kwamitin yana zagayawa, duk bankin da ba zai karbi tsofaffin kudi ba, domin mutane su yi asara, talakawa su yi asara, ‘yan kasuwa su yi asara, mata su yi asara, matasa su yi asara, to za mu soke satifiket din wannan banki.
Idan kuwa mun soke satifiket din wannan banki, to ba su da iko su yi haba-haba a wannan wuri, za kuma mu rushe wannan bankin, za mu zo muyi makaranta yadda za a kara ilmi."
- Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Amfanin canza kudi - Muhammadu Buhari
A baya an ji labari Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce canza manyan Nairori da CBN ya yi zai rage amfani da dukiya wajen lashe zabe a kasar nan.
A jawabin da ya gabatar, Mai girma Buhari ya jero dalilan da suka jawo canza kudi, ya nuna hakan zai bunkasa tattalin arzikin kasa tare da rage tsadar kaya.
Asali: Legit.ng