Ministan Buhari Ya Ɗau Zafi, Ya Caccaki Shugaban Ƙasar Najeriya

Ministan Buhari Ya Ɗau Zafi, Ya Caccaki Shugaban Ƙasar Najeriya

  • Ƙaramin ministan ƙwadago na Najeriya ya caccaki shugaba Buhari kan bijirewar umurnin kotun ƙoli
  • Festus Keyamo yace shugaba Buhari bai fi ƙarfin kotun ba saboda haka ya zama wajibi yayi biyayya ga umurnin ta
  • Ministan ya bayyana cewa shawarar banza aka ba shugaba Buhari kan cewa tsofaffin takardun kuɗi na N200 kaɗai za su cigaba da aiki

Ƙaramin ministan ƙwadago da samar da aikin yi, Festus Keyamo (SAN), ya bayyana cewa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari bai fi ƙarfin kotun ƙoli ba, sannan yakamata ace yayi biyayya kan umurnin kotun akan tsofaffin kuɗi.

Shugaba Buhari ya sanya ƙafa yayi fatali da umurnin kotun a ranar Alhamis lokacin ya sanar da cewa tsohuwar takardar kuɗin N200 za a cigaba da amfani da ita sannan tsofaffin takardun kuɗi na N500 da N1,000 sun dai na aiki.

Kara karanta wannan

"Kana Jawo Kama Tashin Hankali" Gwamna Wike Ya Ɗau Zafi, Ya Aike da Sako Ga Buhari da Atiku Kan Sabbin Naira

Keyamo
Ministan Buhari Ya Ɗau Zafi, Ya Caccaki Shugaban Ƙasar Najeriya
Asali: Twitter

Da yake magana a yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels TV, a ranar Juma'a, Keyamo yace da shine Antoni Janar na ƙasar nan, da ya shawarci shugaba Buhari yayi biyayya kan umurnin kotun ƙoli.

Keyamo yace a ganin shi shugaba Buhari yayi hakan ne ba da niyyar tsallake umurnin kotun ƙoli ba, amma ta iya yiwuwa an bashi shawarar da bata dace ba. Rahoton Channels

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace ba shi bane ya bayar da wannan shawarar domin hakan ba aikin shi bane.

“Ban da masaniya kan wanda ya bashi wannan shawarar . Ina so na faɗi hakan kowa yaji saboda mutane za su riƙa tambaya ta wane ɓangare nake goyon baya a wannan lokacin."

A cewar sa, idan da zai shawarci shugaba Buhari, da ya bashi shawara mai kyau.

"Da ba irin wannan shawarar zan bashi ba. Ba hurumi na bane, ban san wanda ya shawarce shi ba"

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Yi Halinta: An Gano Mutum 2 Da Suka Sauya Wa Buhari Tunani Kan Tawaita Wa'adin N500 da N100

Da aka tambaye shi wacce irin shawara zai ba shugaba Buhari, sai ya kada baki yace:

“Yayi biyayya da umurnin kotun ƙoli wanda yace tsofaffin takardun kuɗi su cigaba da yawo tare da sababbin takardun kuɗi, saboda wannan shine umurnin da kotun ƙoli ta bayar."
“Dole ne hukumomi a Najeriya su yi biyayya ga umurnin kotun ƙoli."

Keyamo yace duk wani abu saɓanin biyayya ga umurnin kotu ƙoli ka jefa ƙasar nan cikin kama karya.

Karya ne: Buhari Ya Gaji, Ya Karyata Zargin El-Rufai da Ganduje na Hana Ayi Zabe

A wani labarin na daban kuma, gwamnatin tarayya ta fito ta ƙaryata raɗe-raɗen da ake yaɗawa kan kafa gwamnatin riƙon ƙwarya a Najeriya.

Lai Mohammed, ministan watsa labarai da al'adu na tarayyar Najeriya shine ya ƙaryata raɗe-raɗin.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida