Ina Bukatar N70m ‘Nakadan’ Domin Hidimin Zabe, Inji Dan Majalisa Ado Doguwa
- Yayin da zabe ya matso, dan majalisar wakilai a Najeriya ya bayyana bukatar a samu kudi don gudanar da aikin zabe
- Ado Doguwa ya koka da cewa, doka ta bashi damar rike N70m kafin zabe, amma bai samu ba
- ‘Yan Najeriya; ‘yan siyasa da gama-gari na ci gaba da kuka kan yadda batun kudi ke kara ta’azzara
FCT, Abuja - Dan majalisar wakilai a matakin tarayya, Ado Doguwa ya bayyana cewa, rashin kudi tsaba a hannu zai shafi zaben 2023 mai zuwa, musamman ga ‘yan siyasa.
A cewarsa, akalla yana bukatar tsabar kudi a hannu da suka kai N70m a lokacin zaben da ke tafe nan ba da jimawa ba, Channels Tv ruwaito.
Ya bayyana wannan batun ne bayan ganawa da shuganan kasa Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Aso Rock a Abuja a ranar Alhamis kan batun ka’idojin kudi.
Doguwa ya shaida cewa, sashe na 88(9) na kudin zabe ya bashi damar samun akalla N70m domin kudanar da harkar zabe, amma bai samu ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kudi nake bukata masu yawa
A cewarsa:
“Ina bukatar tsabar kudi N70m. Wannan shine matsayar doka amma da nake magana daku yanzu bani dasu.”
Ya kara da cewa, wannan ka’idar takaita kudi a hannun jama’a zai shafi ‘yan siyasar da ke neman kujerun takara ba tare da la’akari da jam’iyyarsu ba.
A cewarsa, a wurare da yawa, babu bankuna ko injin ATM don tabbatar da agent-agent da sauran ma’aikatan na zabe sun samu hakkinsu a lokacin zabe, TheCable ta ruwaito.
Dokar nan ta shafi kowa
Ya kuma koka da cewa, wannan dokar ta shafi jam’iyya mai mulki da ma jam’iyyun adawa da ke ‘yan takara a zaben bana.
Da yake martani ga dokar kudi ta CBN:
“Wasu daga cikinmu suna ganin abin alheri game da ka’idar, amma damuwar a matsayinmu na ‘yan majalisa na jam’iyya mai ci shine, meye yasa sai yanzu?”
Doguwa ya jaddada cewa, bai kamata a kawo batun sauyin kudi da sanya ka’idojin kayyade kudi a hannun jama’a ba kwanaki kasa da 40 kafin zabe.
A tun farko, hukumar zabe ta bayyana yadda karancin kudi zai iya shafar zaben 2023 da ke tafe nan ba da jimawa ba.
Asali: Legit.ng