El-Rufai Ya Ajiye Kara, Ya Sake Maka Gwamnatin Buhari a Kotu Saboda Canza Kudi
- Gwamnatin jihar Kaduna za tayi wata shari’a da gwamnatin tarayya a kan batun canza Nairori
- Wannan karo, Abdulhakeem Mustapha ne ya shigar da kara a madadin Gwamnatin Kaduna
- Jihar Arewacin Najeriyar ta zargi gwamnatin tarayya da kin yi wa hukuncin kotun koli biyayya
Abuja - A wani karo na dabam, an fahimci Gwamnatin jihar Kaduna tayi karar gwamnatin tarayya da kuma babban banki na kasa watau CBN a kotu.
Jaridar Aminiya ta ce an shigar da wannan kara a gaban Alkali ne saboda gwamnatin tarayya ta kin yin biyayya ga umarnin kotu a kan karin wa’adi.
Kotun koli ta yanke hukunci cewa a cigaba da amfani da tsofaffin takardu a matsayin kudi kafin a zartar da hukunci a kan karar da wasu jihohi suka kai.
Rahoton ya ce lauyan gwamnati, Abdulhakeem Mustapha (SAN) ya shigar da karar da sunan jihar Kaduna, maganar ta je kotu ne a ranar Litinin dinnan.
Ba ayi wa kotu biyayya ba - Kaduna
A zaman da aka yi a karkashin jagorancin Alkali Inyang Okoro, Barista Mustapha SAN ya ankarar da kotu kan rashin biyayyar gwamnatin tarayya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon Ministan shari’an Najeriya, Kanu Agabi (SAN) wanda ya tsayawa gwamnatin tarayya a kotun, ya musanya duka zargin wannan babban lauya.
Kanu Agabi ya yi kokarin gamsar da Okoro cewa gwamnati ba ta bijirewa umarnin kotu ba.
A gefe guda, kotun ta bada umarni cewa a tanadin bayanan da ake bukata wajen shigar da kara nan da gobe da na gabatar da martani a makon gobe.
A ranar Laraba ake sa ran za a cigaba da sauraron wannan kara domin jin ko gwamnati ta ki yin biyayya ga hukuncin Alkalan kotun kolin kasar.
Ana bugawa a kotun koli
Baya ga wannan kara da ke gaban kotun tarayya da ke Abuja, ana shari’a tsakanin Gwamnonin jihohi da-dama da gwamnatin tarayya a gaban kotun koli.
A kotun koli, Lauyan da ya tsayawa gwamnatin Kano, Sunusi Musa SAN ya nemi alfarma a canza lokacin sauraron shari’arsu da gwamnatin tarayya.
Sanusi II a Kano
A makon yau aka ji labari cewa magoya baya kamar su lashe Mai martaba, Sarki Muhammadu Sanusi II da aka tunbuke a 2020 ya shigo mahaifarsa.
Muhammadu Sanusi II ya nufi zuwa ta'aziyya a Dutse, amma ya ce jirginsa ba zai iya zuwa Jigawa kai-tsaye ba, don haka dolensa sai ya biyo ta jihar Kano.
Asali: Legit.ng