Tashin Hankali Yayin Da Yan Sanda Suka Caka Wa Soja Wuka Suka Kashe Shi A Legas

Tashin Hankali Yayin Da Yan Sanda Suka Caka Wa Soja Wuka Suka Kashe Shi A Legas

  • Mutane suna zaman dar-dar a unguwar Ikorodu a jihar Legas sakamakon mutuwar wani jami'in sojan Najeriya
  • Rahotanni sun nuna cewa wasu jami'an yan sanda ne suka yi sanadin rasuwarsa ta hanyar caka masa wuka
  • Bayan sojan ya rasu ne yan sandan suka gano ashe soja ne duba da cewa ba ya sanye da kayan soja a jikinsa, hakan yasa sojoji sun kona motar yan sanda

Jihar Legas - Hankula sun tashi a unguwar Ikorodu, jihar Legas a yayin da yan sanda suka caka wa wani soja wuka har ya mutu a unguwar.

The Punch ta rahoto cewa lamarin ya faru ne a garin Ogijo da ke tsakanin iyakokin jihar Ogun da Jihar Legas.

Ikorodu
Tashin Hankali Yayin Da Dan Sanda Ya Caka Wa Soja Wuka Kashe Shi A Legas. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Shaidan gani da ido ya magantu kan halaka soja da yan sanda suka yi a Legas

Kara karanta wannan

Karin bayani: El-Rufai ya tona asirin Buhari da CBN kan batun tsawaita wa'adin tsoffin Naira

A cewar rahotanni, yan sandan sun tsere zuwa ofishin yan sanda da ke Ogijo a lokacin da suka ganon wanda suka kashe soja ne.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wata majiya daga unguwar wacce ta zanta da wakilin The Punch ya ce, da kyar ya sha domin mutane suna harbe-harbe a yankin.

Majiyar ta ce:

"Ban iya gane wadanda suke harbe-harben ba domin dare ya faru yi akwai duhu. Lokacin da na sako daga bas, sun fara harbe-harbe kuma kowa ya fara tserewa don neman tsira. Da kyar na sha yau."

Sai bayan da mutumin ya mutu aka gano soja ne, Majiya

Sahara Reporters ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a yankin Odogunyan a Ikorodu.

Wata majiya ta fada wa Sahara Reporters ta rahoto cewa:

"Yan sanda sun kashe sojan ne a yankin Odogunyan, bai saka kayansa na soja ba. Suna gano cewa soja ne, sun tsere zuwa ofishin caji ofis na Ogijo.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Bindige Ɗan Babban Jigon PDP Har Lahira, Bayanai Sun Fito

"Sojojin sun tattaro kansu sun tafi caji ofis sun kona bas (danfo) mallakar yan sanda. Ana ta hayaniya tsakanin hanyar Lagos/Sagamu. Mutane suna ta kokarin tserewa zuwa gida, an rufe shaguna."

Rundunar yan sanda ta kama jami'in soja kan zargin aikata fashi da makami

A wani rahoton daban rundunar yan sandan Najeriya ta jihar Yobe ta cafke wasu mutum uku da ta ke zargi da fashi da makami da hadin baki da balle gida a jihar Yobe.

Cikin mutane ukun da ake zargi har da wani jami'in rundunar soja a da aka ce sun kutsa gidan wata Hajiya Ai'sha Usman wacce ke zaune a unguwar Sabon Pegi a cikin dare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164