Matashi Ya Baje Kolin Cikin Hadadden Gidansa Na Laka Wanda Ya Sha Kayan Alatu a Bidiyo

Matashi Ya Baje Kolin Cikin Hadadden Gidansa Na Laka Wanda Ya Sha Kayan Alatu a Bidiyo

  • Wani bidiyo da ke nuna cikin wani gida da aka gina da laka ya yadu a soshiyal midiya kuma ya haddasa cece-kuce a tsakanin jama'a
  • Mamallakin gidan ya saki bidiyon ne don martani ga wani mutum da ya nemi sanin ko yana da na'urar PS5 a ciki
  • Bidiyon ya hasko cikin gidan lakan wanda aka kawata da kujerun alfarma harda talbijin din bango

Lallai akwai hikimi cikin karin maganar nan da ke cewa fankan-fankan baya kilishi, kuma bidiyon wani gidan laka da ya yadu ya tabbatar da hakan.

Gidajen laka gini ne da suka shahara a zamanin da amma wani matashi ya sauya salon ta hanyar farfado da tsohon gini da sabbin abubuwa na zamani.

Matashi tsaye a gaban gidan laka
Matashi Ya Baje Kolin Hadadden Cikin Gidansa Na Laka Wanda Ya Sha Kayan Alatu a Bidiyo Hoto: @villagehotmen_dripgod
Asali: TikTok

Mutumin ya baje kolin cikin hadaden gidan nasa wanda aka gina da laka don nunawa wani da ya nemi sanin ko akwai na'urar PS5 a ciki ba.

Kara karanta wannan

Babu Wanda Zai Yi Mun Uzuri Saboda Na Auri Mata Har 7, Adam Zango Ya Fadi Dalilinsa Na Cewa Ya Gama Aure

Ya wallafa dan gajeren bidiyo na cikin gidan nasa mai dauke da hadadden kujera na alfarma da kuma hasken wutar lantarki. Bidiyon da ya yadu a TikTok ya nuno lokacin da ya shiga cikin gidan ba tare da riga ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shafi na gaba ya nuno shi yana buga wasan PS5 a tauraron dan adam wato talbijin. Sai dai kuma mutane da dama sun nuna shakku kan bidiyon, suna masu cewa sam bai nuna yadda ya shiga cikin gidan lakan ba.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

big Twink ie / william ya ce:

"Hakan ya tuna mun da fadar cewa abun da ke waje bai da muhimmanci wanda ke cikin shine abun dubawa."

Jamie_England5. ya ce:

"Ka shiga ta kofar a kamara ban yarda cewa gida daya bane."

Kara karanta wannan

Hazikin Dan Najeriya Ya Kera Risho Mai Amfani Da Batura, Bidiyon Ya Dauka Hankali

Tw!zzy ric$ ya ce:

"Ya aka yi da ka shiga cikin gidan ya zama ba gidan laka ba kuma yana dauke da bulo da fari."

[InsertCoolNameHere] ya ce:

"Za mu iya ganin ka kana shiga cikin gidan tukuna? A koda yaushe kaine ka shiga gidan laka mai duhu sannan ka yanka zuwa ciki."

Dan Najeriya ya kera risho mai aiki da batir wajen girki

A wani labarin kuma, wani mutum ya kera rishon girki mai aiki da batir da kuma lantarki kuma baturan kan shafe tsawon makonni biyu kafin ya tashi daga aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel