Sabon salo: Yadda wani mai aski ke kwalkwale kan kwastomominsa da gatari

Sabon salo: Yadda wani mai aski ke kwalkwale kan kwastomominsa da gatari

  • A wani sabon salo, wani mai aski ya wuce iyakar duk yadda mutane ke tsammani da sana'ar aski
  • Ya nemo gatari, inda ya fara aikinsa da yiwa kwastomomi aski da gatari saboda wani dalili
  • Ya bayyana yadda ya faro, da kuma yadda yake fama da kwastomominsa a irin wannan yanayi

Wani mai sana'ar aski daga Kiambu ya shiga kanun labarai bayan da aka gano yana aske gashin kwastomoninsa ta hanyar amfani da kayan aikin da ba a taba tsammanin zai yiyuwa ba.

Julius Mwangi sunansa, kuma yana amfani da gatari ne don aske gashi a shagonsa na aski mai suna Clippers Kings.

Da yake magana da Citizen Digital, Mwangi, wanda ke sana'ar aski tun shekarar 2014, ya ce ya fara aski da gatari ne watanni uku da suka gabata.

Kara karanta wannan

Na yi gyaran kwata ana biya na N20: Ɗan kwallo mafi tsada a Afirka kuma tauraron Super Eagles, Victor Osimhen

Sabon salo: Yadda wani mai aski ke kwalkwale kan kwastomominsa da gatari
Mai sana'ar askin da ke amfani da gatari | Hoto: Citizen Digital
Asali: UGC

Mwangi ya ce ya zabi aski da gatari ne don jawo hankalin sabbin kwastomomi, yana mai bayyana cewa, kuma kwalliya ta biya kudin sabulu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

“Shahararrun mutane suna zuwa akai-akai daga nan na yanke shawarar neman wata hanya ta musamman don jawo hankalin kwastomomi da yin aski cikin nishadi. Ta haka ne na sauka akan gatari."

Yadda yake fama da masu jin tsoron aski da gatari

Mwangi ya yarda cewa yin aski da gatari yana kawo tarin mutane zuwa shagonsa, amma ba kowa bane ke da sha’awar a aske masa kai da gatari ba.

Yace:

“Lokacin da mutane suka ji labarin mai aski da gatari, suna sha'awar sanin a ina. Wasu suna zuwa su gani su dauki hotunan aski da gatari amma sun fi son kada a yi musu aski da shi.

Kara karanta wannan

Ba guduwa zan yi ba: Sheikh Zakzaky ya zargi gwamnatin Buhari da hana shi sakat

"Wasu sukan zo cike da tsoro, amma na kan taimaka musu a shawo kan lamarin."

Fa'idojin amfani da gatari wajen aski

Mwangi ya bayyana cewa aski da gatari yana da wasu fa'idodi fiye da na injin aski.

A cewarsa:

“Gatari yana ba da aski mai laushi wanda ya fi dacewa da salon askin Jordan. Haka kuma, lokacin da aka dauke wuta, na kan ci gaba da aikina kamar yadda na saba.”

Mai askin ya kuma bayyana cewa gatari ya fi dacewa da aski ga kwastoman da ke da cikakken gemu.

Shin ko yana da wani shiri nan gaba?

Mwangi ya bayyana shirinsa, yana mai cewa:

“Ina neman gatari mara nauyi saboda wannan yana da nauyi kadan. A halin yanzu ina karbar KSh 500 (N1,848) a aski amma farashin zai tashi daidai da bukata.”

Martani a kafar sada zumunta

David Nyaga Njeru:

"Ba zan iya daukar wannan hadarin ba har haka. Ina son kaina da wuyana."

Kara karanta wannan

Tsoho mai shekaru 60 ya kashe ɗansa mai shekaru 32 saboda saɓani da ya shiga tsakaninsu

Gatimu Robert:

"Wannan mutumin ya kware a fasaha, ba kowa ne zai iya ba."

Mwangi Njenge Inv:

"Kyakkyawar dabarar kasuwanci."

Titus Kimathi Marangu:

"Ba zan iya amincewa da wani mutum ya aske gashin wayayyen kaina ta amfani da makami ba."

Yadda tsoho mai shekara 72 ya ginawa matarsa abar kaunarsa gida mai jujjuyawa

A wani labarin kuwa, wani mutum ya kai kololuwa wajen farantawa matar sa rai wanda a ko da yaushe take korafin ginin gidansu ta hanyar gina mata gida mai juyawa.

Vojin Kusic mai shekaru 72 daga Bosnia ya zana salon gidan ne daga fikirar masu kirkirar Sabiya-Amurka Nikola Tesla da Mihajlo Pupin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel