Mutane Hudu Sun Mutu Yayin da Zanga-Zanga ta Tsananta a Jihar Edo

Mutane Hudu Sun Mutu Yayin da Zanga-Zanga ta Tsananta a Jihar Edo

  • Mutane huɗu aka tabbatar da sun mutu a wurin zan-zangar da ta barke a gaban hedkwatar CBN dake Benin jihar Edo
  • Bayanai sun nuna cewa yan sanda na bakin kokarinsu wajen tarwatsa tulin masu zanga-zanga da hana su shiga CBN
  • Fusatattun yan Najeriya sun fara zanga-zanga a sassan ƙasar nan kan karancin naira da daina amfani da tsoffi

Edo - Akalla mutane huɗu aka tabbatar sun mutu yayin da rikici ya ƙara tsananta a Benin, babban birnin jihar Edo kan tsarin sauya fasalin naira da CBN ya ɓullo da shi.

The Nation tace waɗanda suka mutu na cikin tulin Kwastomomin bankuna waɗanda suka yi kokarin maida tsoffin takardun kuɗinsu reshen CBN dake Titin Akpakpava, Benin.

Zanga zanga a Edo.
Mutane Hudu Sun Mutu Yayin da Zanga-Zanga ta Tsananta a Jihar Edo Hoto: thenation
Asali: UGC

Biyu daga cikin mamatan matasa ne sai kuma mace ɗaya da harsashin yan sanda ya yi ajalinta a gaban hedkwatar CBN reshen jihar Edo.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Fusatattun Mutane Sun Bankawa Bankuna da ATM Wuta Kan Karancin Naira

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an yan sanda sun harba barkono mai sa hawaye domin tarwatsa dandazon mutanen da suke zanga-zangan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ɗaya daga cikin masu zanga-zangan, wanda yaƙi bayyana sunansa, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa sun ga gawarwakin mutane huɗu a gaban CBN, cikin sauri 'yan sanda suka kawar da uku.

Ya ƙara da cewa waɗanda suka je maida tsoffin kuɗin ne suka hana a ɗauke gawa ta hudun, wani matashi da bai wuce shekaru 20 ba a duniya.

Sojoji da 'yan sanda ɗauke da makamai ne suka hana masu zanga-zangar matsa wa kusa da babbar ƙofar shiga CBN.

Sakamakon haka ne masu zanga-zangar suka ƙara fusata, suka nufi bankunan kasuwanci da ke kusa da wurin suka yi kaca-kaca da su.

Yan sanda sun yi harbe-harbe

Wata motar sulken yan sanda mai lamba NPF 3200 D ce ta jagorancin wasu Motocin sintiri zuwa wurin da zanga-zangar ta barke.

Kara karanta wannan

Labari Mai Daɗi: Buhari Ya Canza Shawara, FG Da CBN Zasu Duba Yuwuwar Tsawaita Wa'adin Naira

Rahoto ya nuna cewa jami'an sun buɗe wa mutane wuta kana suka koma harbin iska yayin da masu zanga-zangar suka bi motocin da jifa da duwatsu.

Mafi yawan manyan Titunan Benin da kewaye masu zanga-zanga sun toshe su, matafiya kuma sun rika sanya Ganye a motocinsu domin gudun farmaki da nuna ana tare.

A wani labarin kuma Fusatattun Mutane Sun Bankawa Bankuna da ATM Wuta Kan Karancin Naira a Jihar Delta

Karanci sabbin kuɗi da kuma daina karban tsaffi a sassan Najeriya sun harzuka mutane, sakamakom haka wasu suka barke da zanga-zanga dan nuna fushinsu.

A jihar Delta, gwamna Okowa ya yi kira ga mutane su kwantar da hankulansu domin masu alhaki kan lamarin na kokaren share masu hawaye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262