Gwamnan Bankin CBN Ya Bayyana Inda Sababbin Kudin da Aka Buga Suka Shige

Gwamnan Bankin CBN Ya Bayyana Inda Sababbin Kudin da Aka Buga Suka Shige

  • Ganin zaben 2023 ya zo daf, Godwin Emefiele ya ce wasu ‘Yan siyasa ne suke boye sababbin kudi
  • Gwamnan babban bankin Najeriya ya yi bayanin nasarorin da aka samu a dalilin canza kudi
  • Emefiele ya ce a yau farashin abinci ya sauka a kasuwa, kuma an natsar da kasuwar canji

Abuja – Gwamnan babban banki, Godwin Emefiele ya ce sun lura wasu ‘yan siyasa su na sayen sababbin N200, N500 da N1000 domin manufar siyasa.

Arise ta ce a yayin da Godwin Emefiele ya zanta da manema labarai ranar Talata, ya shaida masu ‘yan siyasa sun tattara takardun kudin da aka buga.

Gwamnan na CBN yake cewa ‘yan siyasar su na yin haka ne saboda a soki tsarin da ya fito da shi.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, a jawabin da ya yi, Emefiele ya roki mutane su bada hadin-kai wajen ganin an dabbaka tsarin takaita yawon kudi.

Kara karanta wannan

Matsayar Tinubu, Atiku, Kwankwaso da Obi a kan batun Canjin N200, N500 da N1000

Mugun nufin 'Yan siyasa

"Bankin CBN ya kuma fahimci wasu ‘yan siyasa su na sayen sababbin takardun kudin, su na boye su saboda manufofin siyasa."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

- Godwin Emefiele

Bankin CBN
Bankin CBN a Abuja
Asali: Twitter

The Cable ta rahoto Emefiele yana cewa tun farko an fito da tsarin ne da nufin bunkasa tattalin arziki, a cewarsa yanzu farashin kaya ya fara sauka.

Baya ga haka, Gwamnan babban bankin ya ce an soma ganin cigaba a wajen darajar Naira. A cikin manufar tsarin shi ne a rage yawan marasa aiki da banki.

Farashin kaya a kasuwannin Suleja da Lambata sun nunawa CBN an samu raguwar tsadar waken suya, masara da sauran kayan abinci har zuwa dabbobi.

Da yake magana a gaban mutanen kasar waje, an ji Gwamnan yana cewa a ketare mutane ba su yawo haka kurum kudi, ana cafke duk wanda aka kama.

Kara karanta wannan

Dalilin Canza Kudi, Mai Martaba Ya Koka da CBN, Babu N20, 000 a Cikin Fadar Sarki

Akwai hannun Gwamnoni 10

Obed Okwukwe ya shaidawa Duniya akwai wasu Gwamnonin jihohi 10 da suka tattara kudin da aka buga, sun dage cewa sai tsarin nan ya daina aiki.

A cewar Okwukwe, CBN ya raba Naira biliyan a karon farko, amma ana zargin yanzu wadannan kudi ba su bar bankuna, sun shiga hannun talakawa ba.

Kutun-kutun ne - Gbaja

A wani rahoto, an ji labari cewa Femi Gbajabiamila wanda shi ne Shugaban majalisar wakilan tarayyan kasar ya ce sauya kudi tsari ne mai kaifi biyu.

Rt. Hon. Gbajabiamila yana ganin Bola Tinubu ake yaka da sunan canza kudi saboda a hana shi lashe zabe, ya kuma ce dabarar ba tayi aiki da kyau ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng