Ba Zan Iya Tafiya Da Shi Gida Ba: Budurwa Ta Saki Bidiyon Mahaifinta Mai Lalurar Tabin Hankali

Ba Zan Iya Tafiya Da Shi Gida Ba: Budurwa Ta Saki Bidiyon Mahaifinta Mai Lalurar Tabin Hankali

  • Jama'a sun yi cece-kuce bayan bayyanar bidiyon wata matashiyar budurwa yar Najeriya tana taya mahaifinta mai lalurar tabin hankali murna
  • Matshiyar ta saki bidiyonta tana wasa da mahaifinta sannan tana taka rawa tare da shi yayin da ya kara shekaru a doron kasa
  • Mutumin wanda ke sanye da tsummokara yana murmushi yayin da kyakkyawar diyar tasa ke raya wannan rana tare da shi

Lokaci zuwa lokaci, yan kananan abubuwan da mu kan yi wa juna ya kan nuna kyawun da ke tattare da rayuwar duniya, musamman a ranakun bazdai dinmu.

Wata kyakkyawar matashiya yar Najeriya ta yi kyan kai wajen taya mahaifinta wanda ke fama da lalurar tabin hankali murnar kara shekaru a duniya.

Diya da mahaifinta
Ba Zan Iya Tafiya Da Shi Gida Ba: Budurwa Ta Saki Bidiyon Mahaifinta Mai Lalurar Tabin Hankali Hoto @amokeceleb4
Asali: TikTok

Wani hadadden bidiyo ya nuno ta tana taka rawa tare da mahaifin nata sannan ta ware lokaci a kokarinta na taya shi murna.

Kara karanta wannan

Ba Zan Tashi a Tutar Babu Ba: Uwar Biki Ta Fito Da Lambar Akant a Wurin Liyafar Bikinta, Ta Ce kowa ya Tura Mata Kudi

Cike da alfahari, ta wallafa bidiyon a TikTok don nunawa duniya don su yi masa addu'a.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Koda dai bai kasance cikin shiga mai kyau ba, ya kasance dauke da murmushi a fuskarsa wanda ke nuna farin cikin dan yake ciki har zuciyarsa.

Babban n'ima ne ace mutanen da kake matukar so a rayuwa suna tunawa da kai. Diyar tasa ta kawo masa wasu yan kyaututtuka a bidiyo sannan sun yi hotuna tare.

Da suke martani ga bidiyon, wasu jama'a sun caccaki matashiyar a kan kin tafiya da mahaifin nata gida don sauya masa tufafin jikinsa.

Matashiyar ta amsa a sashin sharhi cewa ta yi kokarin aikata hakan amma ya ki bin ta gida.

Jama'a sun yi martani

@treasurekiss13 ta ce:

"Barka da zagayowar ranar haihuwarka yallabai."

@tailormafia ta ce:

"Ki yi abun da ya fi dacewa ga mahaifinki, ina taya mahaifinki murnar zagayowar ranar haihuwarsa. Ki sa mahaifinki ya fi haka kyan gani."

Kara karanta wannan

Bidiyon Budurwa Tana Murna Bayan Saurayinta Ya Kai ta SIyan Gwanjo Kafin Zuwa Ranar Masoya ta Duniya

@barbielora107 ta ce:

"Dan Allah ba za ki iya tafiya da shi gida ba idan har za ki iya yin hotuna tare da shi."

A wani labarin, wata matashiyar budurwa ta nuna bacin ranta bayan ta mika kokon barar soyayyarta a gaban wani matashi amma ya ce baya yi.

Ta dai hadu da shi ne a soshiyal midiya kuma ta ji ya yi mata ammma ya ce shi yana da budurwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel