Ganduje ya Bayyana Matakin da Zai Dauka kan Bankuna da ‘Yan Kasuwa Masu Kin Karbar Tsofaffin Kudi

Ganduje ya Bayyana Matakin da Zai Dauka kan Bankuna da ‘Yan Kasuwa Masu Kin Karbar Tsofaffin Kudi

  • Gwamnatin jihar Kano ta yi kira da kakkausar murya ga 'yan kasuwan da ke cigaba da kin amincewa da tsoffin kudi a kasuwancinsu
  • Gwamnan jihar ya ce ba zai yi kasa a guiwa ba wajen kwace lasisin kasuwanci da daukar matakin da ya dace ga duk 'dan kasuwan da ya ki amincewa da tsoffin kudi a kasuwancinsa ba
  • Ya kara da cewa, kin amincewa da tsoffin kudi a wasu bata gari masu son zuciya ke yi shi ne ke assasa tsananin rayuwar da dokar sauya fasalin kudin ta jefa jama'a

Kano - Gwamnatin jihar Kano ta yi jan kunne cewa, ba za ta yi kasa a guiwa wajen kwace lasisin kasuwancin ko daukar mataki ga duk 'dan kasuwan da ya ki amsa tsoffin kudi a kasuwancinsa ba.

Kara karanta wannan

Rudani: Kotuna sun ki karbar tsoffin Naira duk da kuwa kotun koli ta ce a ci gaba da karba

GanDuje
Ganduje ya Bayyana Matakin da Zai Dauka kan Bankuna da ‘Yan Kasuwa Masu Kin Karbar Tsofaffin Kudi. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya yi jan kunnen a wata takarda da kwamishinan watsa labarai da lamurran gida, Malam Muhammad Garba ya fitar, ya ce har yanzu tsoffin kudi basu daina amfani ba, Channels TV ta rahoto.

A cewar, Kotun Koli ta tausaya, inda tasa dokar wucin gadi game da tsoffin kudi wadanda za a cigaba da amsa tare da sabbi har sai sun kare.

Gwamnan ya bayyana yadda gwamnati ta gano yadda 'yan kasuwa irinsu kantina, shaguna, bankuna, wuraren sai da abinci, gidajen saukar baki, masu saide-saide a kasuwanni, gidajen mai, wuraren aje motoci, da sauransu suka dauki dabi'ar kin amsar tsoffin kudi a kasuwancinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta rahoto cewa, Haka zalika, Ganduje ya lura cewa, kin amsar da wasu mutane masu son kan zuciya suke ke cigaba da assasa lamarin da ya riga ya yi kamari da karancin sabbin kudi.

Kara karanta wannan

Sokoto: Gidajen Mai, Yan Kasuwa Da Bankuna Sun Dena Karbar Tsaffin Takardun Naira

"Kasuwancin da ayyukan tattalin arziki sun matukar cutuwa da sauya fasalin kudin da aka yi, sai dai, abun takaici shi ne yadda wasu mutane masu son zuciya ke cigaba da assasa tsananin rayuwar kan mutane ta hanyar kin amsar tsoffin kudi yayin kasuwanci,"

- Kamar yadda takardar ta kara.

A cewarsa, mutane sun ji a jikinsu wanda ba sai an fadi ba, don haka gwamnatin jihar baza ta sa ido ta bar wasu kalilan din bat—gari su antaya wa wutar fetur ba.

Gwamnan ya yi kira ga kafatanin mutanen jihar da su cigaba da kasuwancinsu, tare da kai karar duk wanda ya ki amsar tsoffin kudi ga hedkwatocin da suka dace.

Bankuna sun yi fatali da umarnin kotu, sun daina karbar tsofaffin kudi

A wani labari na daban, bankunan ‘yan kasuwa a wasu jihohin Najeriya sun daina karbar tsofaffin takardun N200, N500 da N1,000.

Bankunan sun bayyana cewa, babban bankin Najeriya aka maka a kotu ba su ba, don haka sai sun samu umarni daga can.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng