Daruruwan Yan Najeriya Sun Yi Layi Don Cire Kudi Da Karfe 2 Na Tsakar Dare a Fadin Kasar

Daruruwan Yan Najeriya Sun Yi Layi Don Cire Kudi Da Karfe 2 Na Tsakar Dare a Fadin Kasar

  • Yanzu yan Najeriya na zuwa cire kudi da tsakar dare domin gudun tarar da dogon layi a rumfar ATM
  • Sabon tsarin babban bankin Najeriya ya jefa rayuwar yan Najeriya mazauna birni da karkara cikin kunci
  • A halin yanzu, daruruwan yan Najeriya sun koka kan yanayin da ake ciki, inda da dama suka bayyana halin da suka shiga

A yanzu yan Najeriya na kwana ne a gaban rumfunar na'urorin ATM din bankuna daban-daban domin samun damar cire sabbin kudi.

A wani sabon bidiyo da aka yada a Facebook, wani mutumi da ya nadi bidiyon ya bayyana yadda ya ga daruruwan mutane a rumfunar ATM daban-daban kan layi da misalin karfe 2:00 na tsakar dare.

Layin ATM
Daruruwan Yan Najeriya Sun Yi Layi Don Cire Kudi Da Karfe 2 Na Tsakar Dare a Fadin Kasar Hoto: CKN
Asali: Facebook

Rahotanni sun nuna cewa bisa tilas, mutane da dama sun yi layi na tsawon awanni biyar don kawai su samu cire kudi, wanda ba zai wuce N20,000 ba a kullun.

Kara karanta wannan

Mafita ta samu, CBN ya fadi hukuncin da zai yiwa masu POS da ke karbar sama da N200

Bidiyon ya haifar da martani da dama. A halin da ake ciki, yan Najeriya sun yi martani a kan lamarin yin layi gaban ATM da sakar dare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Martanin jama'a kan halin da ake ciki

Tony James:

"Da misalin karfe 2:00 na tsakar daren yau a VI, mutane kan layi don karbar kudinsu daga ATM kuma haka abun yake a ko'ina a cikin gari kowani dare. Abun bakin ciki. Shin akwai wani buri a kasar nan kuma?"

Soromtobechukwu Ozoh

"Ban san wani laifi yan Najeriya suka aikata da suke fuskantar irin wannan kalubalen ba. Karfe 00:31, har yanzu akwai mutane a gaban ATM. Ni ne lamba na 33. Idan ba cire kudi yau ba, ba lallai tafiyana ya yiwu yau ba. Wani ya fada mun cewa sun zuba kudi da karfe 2:00 na tsakar dare da 6:00 asubahi.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: 'Yan sanda sun dauki mataki kan faston da aka ga ya rataye AK-47 a Abuja

"Don haka mutane da ke sane, musamman masu POS, suna zuwa ne da karfe 12/1 na tsakar dare. Safiyar kiya a hanyana na zuwa coci, na gamu da dogon layi a bankin Union a yankin low cost. kamar wadannan mutanen sun kwana ne a waje, don kawai su samu kudin gudanar da harkokinsu."

Kissinger Ikeokwu

"Na farka da 4:00 na asubahi don karbar kudi daga ATM tun da sun ce ta nan ne kawai mutum zai samu sabbin kudin. Da shigana gari sai na ga cewa na yi latti ma. Mutane sun rigada sun bazama daga wannan bankin zuwa wancan bankin don neman karbar 20k dinsu. Kai.
"Labari mara dadin shine cewa kaso 98 na banki/ATM a Owerri basu da kudi ko basu da sabis.
"Na ji cewa mutane sun shafe tsawon dare a bankin da ke da kudi har 2:00 na tsakar dare. An fada mani cewa sai da mai gadin bakin ya fatattaki mutane don rufe rumfar ATM dinsu da ake amfani da shi 24/7. Da safen nan, layin da na gani ya sa nayi da nasanin me ya hana ni biyan 1k don karbar 10k a kasuwan bayan fage a jiya. Eh. Ba zan iya shan wahala wajen karbar kudina ba."

Kara karanta wannan

Sanatan APC Ya Fadi Wanda Zai Zama Babban Kalubale Wajen Shirya Zaben 2023

Yan Najeriya sun yi zanga-zanga a CBN, sun bukaci a sauya masu tsoffin kudinsu

A wani labarin, wasu yan Najeriya sun yi zanga-zanga a CBN reshen Edo inda suka nemi lallai babban bankin ya sauya masu tsoffin kudinsu don bankunansu sun ki karba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel