Rikici a Najeriya Yayin da Kotuna Suka Ki Karbar Tsoffin Takardun Naira

Rikici a Najeriya Yayin da Kotuna Suka Ki Karbar Tsoffin Takardun Naira

  • Yayin da umarnin kotu yake kasa, bankuna da hukumomin gwamnati sun daina karbar tsoffin Naira
  • Kotunan jihar Legas sun ce ba za su karbi tsoffin kudi ba saboda bankuna sun daina ta’ammuli da kudaden
  • Mazauna a jihar Gombe sun koka kan yadda aka ki karbar tsoffin kudi da kuma yadda ake ba su kananan kudi

Jihar, Legas - An samu tsaiko a jihar Legas a ranar Litinin yayin da wasu manyan kotunan jihar suka ki karbar tsoffin Naira daga hannun lauyoyi da masu shigar da kara.

Jami’an da ke aiki a kotunan sun ki karbar tsoffin kudin tare da cewa, bankuna sun daina karbar kudin a halin da ake ciki.

Wannan sabon lamari ya zo da tsaiko yayin da kasar ke kara fuskantar karancin sabbin kudin da CBN ya buga a kwanakin baya.

Kara karanta wannan

Sokoto: Gidajen Mai, Yan Kasuwa Da Bankuna Sun Dena Karbar Tsaffin Takardun Naira

Kotuna sun daina karbar tsoffin kudi
Rikici a Najeriya Yayin da Kotuna Suka Ki Karbar Tsoffin Takardun Naira | Hoto: David Darius
Asali: Getty Images

Yadda aka kaya tsakanin ma’aikatan kotu da lauyoyi da masu shigar da kara

Akawun kotunan tsibirin Legas da na Ikeja sun bayyana cewa, dole masu shigar da karan da kuma lauyoyi su ba da sabbin kudade, inda suka ce sun yi kokarin sanya tsoffin kudi a asusun gwamnati amma abu ya gagara.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani ma’aikacin kotun Ikeja da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, mai gidansu a wurin aiki ya ba su umarnin cewa kada su sake karbar tsoffin kudi.

Da yake bayyana hujjarsa, ya ce kotun ya dauki tsoffin kudi don kai wa bankunan FCMB, Polaris, UBA da Fidelity amma an ki karba.

Jami’in kotun ya kuma bayyana cewa, don haka dole ne lauyoyi da masu shigar da kara su zo da sabbin kudi don gujewa asara.

Lauya ya magantu

Kara karanta wannan

Bankuna Sun Fatali da Umarnin Kotu, Sun Ce Bazasu Karba Tsofaffin Kudi ba, Sun Sanar da Dalilansu

Daya daga cikin lauyoyin da abin ya shafa ya shaidawa jaridar Punch cewa, kotun Osborne na jihar Legas ya ki karbar tsohon kudi daga hannunsa lokacin da ya zo shigar da wata kara.

Ya koka da cewa, an yi biris da umarnin kotun koli na barin tsoffin kudi su ci gaba da yawo a hannun jama’a.

Idan baku manta ba, a ranar 8 ga watan Faburairu ne kotun kolin ya umarci CBN da ya bari a ci gaba da amfani da tsoffin kudi har zuwa lokacin da zai sake zama a ranar 15 ga watan Faburairu.

Sai dai, binciken da Legit.ng Hausa ta yi ya nuna cewa, bankuna, shagunan siyayya da sauran kasuwa sun daina karbar kudin tun ranar 11 ga watan Faburairu.

An daina karbar tsohon kudi

A ziyarar da wakilinmu ya kai bankin Stanbic IBTC da ke jihar Gombe, ya gaza shiga bankin saboda layi, ga kuma kwastomomi sun gaza shigar da tsoffin kudadensu.

Kara karanta wannan

Sabon ciwon kai ga 'yan Najeriya: Wasu bankuna sun daina karbar tsoffin Naira

Muhammad Yunusa, wani dan kasuwan da ya tattaro tsoffin kudinsa ya kawo ya ce:

“Ba sa karbar tsoffin kudi, domin yanzu abokina ya tafi ba a karbi nasa ba. Na tsaya ne saboda na yi waya da abokina ma’aikacin bankin ya ce zai san yadda za a yi.”

A gefe guda, Sadiq Adamu, wani kwastoman da ke sana’ar POS da ya ciro kudi daga bankin ya ce:

“A da mu ‘agent’ ana ba mu N200,000, amma yanzu N20,000 ake ba mu, ka gansu, tsoffin ‘yar N10 ne, me zan yi dasu?”

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.