Karancin Naira: Gwamnan Neja Ya Maka Gwamnatin Tarayya a Kotu Yayin da Kasuwannin Karkara Suka Rufe

Karancin Naira: Gwamnan Neja Ya Maka Gwamnatin Tarayya a Kotu Yayin da Kasuwannin Karkara Suka Rufe

  • Gwamnatin jihar Neja ta shiga jerin jihohin da suka maka gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a gaban kotu kan manufar sauya kudi a kasar
  • Jihar Neja ta bukaci kotun koli ta sa CBN kara wa'adin daina amfani da tsoffin kudi da komawa ga sabbin N200, N500 da N1,000
  • Ta ce wannan manufa na CBN ya jefa al'ummar jihar musamman mazauna karkara cikin kangin rayuwa yayin da harkokin kasuwanci suka tsaya cak

Niger - Gwamnatin jihar Neja ta shigar da karar gwamnatin tarayya a gaban kotun koli kan manufar sauya takardun Naira na babban bankin Najeriya (CBN), jaridar The Guardian ta rahoto.

A wata sanarwa daga Atoni Janar kuma kwamishinan shari'a na jihar, Justis Nasara Danmallam, a ranar Asabar, 11 ga watan Fabrairu, ya ce an shigar da karar mai lamba SC/CV/210/2023, a ranar 10 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

An Samu Jihar APC ta 5 da ta Shigar da Karar Gwamnatin Buhari a Dalilin Canza Kudi

Justis Danmallam ya kuma ce gwamnatin jihar Neja ce mai shigar da kara a cikin shari'ar.

Gwamna Sani Bello
Karancin Naira: Gwamnan Neja Ya Maka Gwamnatin Tarayya a Kotu Yayin da Kasuwannin Karkara Suka Rufe Hoto: Thisday
Asali: UGC

Rashin sabbin kudi ya jefa al'ummar Neja cikin kangin rayuwa

Sanarwar ta ce gwamnatin jihar na neman a kara wa'adin da CBN ya bayar don sauya sabbin kudi da daina amfani da tsoffin takardun kudi yan N200, N500 da N1,000.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Har ila yau, ta ce watanni uku da gwamnatin tarayya ta bayar don janye tsoffin kudi a fadin kasar bai dace ba kuma ya saba wa sashi na 13, 14 (2) (b), 17 (1) (c) na kundin tsarin mulkin 1999.

Bugu da kari, gwamnatin ta jihar Neja ta ce rashin sabbin kudi ya jefa mutane cikin wahala da kangin rayuwa a jihar, musamman wadanda ke zama a yankunan karkara.

Sanarwar ya nuna damuwar gwamnatin jihar game da matsin da manufar sauya takardun Naira ya jefa mutane a ciki, cewa gwamnatin za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa bisa tanadin kundin tsarin mulki don magance wahalar da suke ciki.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Kano Ta Maka Gwamnatin Tarayya A Kotu Kan Sauya Fasalin Naira, Ta Bada Dalili

Harkoki sun tsaya cak a kasuwannin karkara saboda rashin sabbin kudi

Jaridar Leadership ta rahoto cewan yawancin kasuwannin karkara sun rufe harkoki saboda rashin sabbin kudi da kuma rashin tabbass dangane da wa'adin daina karbar kudin.

An lura cewa kasuwannin abinci, awaki da na kifi a Zumba, Mariga da Chimbi basu yi harkoki yadda ya kamata ba saboda rashin tsabar kudi.

Bincike ya nuna cewa wasu masu siyar da kayayyaki kamar su doya, dankali, hatsi da kayan lambu basu siyar da kayayyakinsu ba saboda ba za su iya karbar kudi ta asusun kai tsaye ba.

Wakiliyar Legit.ng ta leka kasuwar Gwadabe da ke garin Minna wanda ke ci duk ranar Asabar inda ta gan shi ya yi yara-yara babu mutane sosai.

Wani mai sana'ar kayan hatsi a kasuwar ya ce hakan baya rasa nasaba da rashin kudi a gari domin hatta tsoffin kudaden ya ce babu su a yanzu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Buhari ta Bukaci Kotun Koli Tayi Watsi Da Karar Gwamnonin Da Suka Shigar Kan Tsaffin Naira

Ya ce:

"Kamar yadda kika gani yau babu cunkoson jama'a kuma ma ai sai da kudi ake shiga kasuwa, babu abun da za mu ce a wannan lokaci sai dai Allah ya kawo mana sauki, amma dai ana cikin yanayi.
"Ga dai kaya mun kawo amma babu masu siya saboda rashin kudi, mu kuma karbar transpa dinnan yana da matukar hatsari a bangarenmu, don yanzu cuta ta yi yawa."

Jihohin arewa 3 sun maka CBN da Buhari a kotu

A baya mun ji cewa yayin da ake ci gaba da fama da rashin wadatar kudi a kasar, gwamnatocin Kogi, Kaduna da Zamfara sun maka gwamnatin tarayya da CBN a gaban kotun koli.

Sun bukaci a hana CBN aiwatar da wa'adinsa na daina amfani da tsoffin takardun kudi a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng