Uwar Jam'iyyar PDP Ta Sallami Sanatanta, 'Dan Fayose, Saboda Suna Goyon Bayan Tinubu
- Jam'iyyar PDP ta dauki mataki mai tsauri kan wasu 'yayanta da suke mata zagon kasa
- Babba ciki shine daya daga cikin wadanda suka kafa jam'iyyar a 1999, Sanata Chimaroke Nnamani
- Sanatan ya ce ba'a yi masa adalci ba saboda ko sau daya ba'a kira sa aka fada masa laifin da yayi ba
Abuja - Uwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta sallami Sanata Chimaroke Nnamani, dan majalisar dattijai mai wakiltar yankin Enugu ta yamma.
A jawabin da Kakakin PDP, Debo Ologunagba, ya fitar, jam'iyyar ta ce ta yanke shawaran fitittikar Nnamani ne bayan zaman majalisar gudanarwarta na 566 ranar Juma'a a Abuja.
Ya ce an sallami Nnamani da wasu mutum shida ne bisa yiwa jam'iyyar zagon kasa wanda ya saba kundin tsarin mulkin jam'iyyar.
Sauran wadanda aka sallama sun hada da Chris Ogbu (Imo), Ajijola Lateef Oladimeji (Ekiti), Olayinka James Olalere (Ekiti central II), Fayose Oluwajomiloju John (Ekiti central I), Akerele Oluyinka (Ekiti north I), da Emiola Adenike Jennifer (Ekiti south II).

Asali: Twitter
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewarsa:
"Shawarar da NWC ta yanke ya biyo bayan shawarar kwamitin ladabtarwa bisa sashe na 58 and 59 (1)(g) na kundin tsarin mulkin PDP."
"Jam'iyyar PDP na kira ga dukkan mambobin jam'iyyarmu a fadin kasa su kasance tsintsiya madaurinki daya don ceto da gyara kasar nan daga hannun shugabanni mara kwarewa."
Nnamani ya yi martani
Sanata Chimaroke Nnamni ya yi martani kan labarin fittikarsa da jam'iyyasr PDP tayi.
Ya bayyana cewa ba'a yi masa adalci ba kuma ba'a sanar da shi dalilin da yasa aka koreshi ba.
A jawabin da ya fitar a shafinsa na Tuwita, ya bayyana sassa na kundin tsarin jam'iyyar.
Ya ce:
"Ko sau daya ba'a sanar da ni akwai wani laifi da nayi ba kuma ba'a sanar da ni dalilin dakatar da ni daga jam'iyyar ba."
"Ba'a gayyace ni wani zama ko ganawa na NWC ba inda ya kamata a tattauna laifi na ba. Saboda haka ba'a bani damar kare kaina ba."
Asali: Legit.ng