Gwamnati Ta Hana Gasa Kifi Da Nama A Kasuwannin Jihar Abia

Gwamnati Ta Hana Gasa Kifi Da Nama A Kasuwannin Jihar Abia

  • Gwamnatin Jihar Abia ta saka dokar hana gasa kifi da nama da yin girki a manyan kasuwannin jihar
  • Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar ya saka wannan dokar ne bayan afkuwar wata gobara sakamakon barin risho da wata mai gasa kifi ta yi a kunne
  • Gwamnatin jihar na Abia ta yi kira ga shugabannin kasuwanni su tabbatar an aiwatar da dokokin kiyayye gobarar da gwamnatin ta saka

Jihar Abia - Gwamnan jihar Abia Okezie Ikpeazu jihar ya bada umurnin hana gasa kifi da wasu dabobi da girki a cikin manyan kasuwannin jihar, rahoton jaridar Leadership.

Hakan ya biyo bayan gobarar da ta faru a ranar 8 ga watan Fabrairu, a line 27 off Ngwar road market, wanda ya shafi shaguna biyu.

Idan za a iya tuna wa gobarar ya tashi ne sakamakon risho da mai gasa kifi ta bari a kunne bayan ta tashi aiki, kamar yadda Nigerian Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: 'Yan Bindigan da Suka Yi Garkuwa da Kwamishina Sun Turo Sako Mai Ɗaga Hankali

Gashin Kifi
Gwamnatin Abia Ta Hana Gasa Kifi Da Wasu Dabobi A Kasuwa. Hoto: The Guardian
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar da kwamishinan kasuwanci da saka hannun jari, Cif John Okiyi Kalu ya fitar ta ce, Gwamna Okezie Ikpeazu, ya umurci ma'aikatar kasuwanci da saka hannun jari ta bincika asarar da aka yi a gobarar da nufin tallafa musu, rahoton The Guardian.

Gwamnatin Abia za ta bada tallafi ga yan kasuwar da gobarar ta shafa

Wani sashi na sanarwar ya ce:

"Yayin da muke gode wa Allah cewa jami'an kasuwa da sauran mutane sun taimaka wurin kashe gobarar, Gwamna Ikpeazu ya umurni ma'aikatar kasuwanci da saka hannun jari da lissafa asarar da aka yi a shagunan biyu da nufin tallafa musu.
"Muna kira da dukkan shugabannin kasuwanni su aiwatar da dukkan dokokin kare gobara a kasuwannin mu ciki har da tabbatar da cewa ba a bari an ajiye abin da ke saurin kama wa da wuta ba a kasuwanni da raba na'urar kashe gobara."

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Na San Yadda Zan Yadda Zan Gyara Tattalin Arzikin Najeriya, Bola Tinubu

Mata yan gidan magajiya sun magantu yayin da gwamnatin jihar Neja ke shirin haramta 'sana'arsu'

A wani rahoton da muka kawo kun ji cewa gwamnatin jihar Neja ta ce za ta haramta karuwanci a wani yunkurin inganta tsaro a jihar.

Famanan sakatare na ma'aikatar ayyukan cigaba da mata na jihar Kaltum Rufai ne ta sanar da hakan yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164