Matashi Mai Tallan Asusun Gwangwani Ya Sanya Masu Suna Zenith, Kuda Da Sauran Bankuna
- Wani matashi ya sha jinjina a soshiyal midiya saboda hazikanci da ya nuna wajen daga darajar asusu da sunayen bankunan Najeriya
- Mutane da dama da suka yi martani ga bidiyon sun bayyana cewa kasar nan ta yi wuya kuma shi din yana kokarin ganin yadda zai rayu a cikinta ne
- A TikTok, wasu masu amfani da soshiyal midiya sun ce suna neman sunayen bankinsu a kan kowani asusu
Wani mai tallan asusu da aka kera da gwangwani ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya. Wasu rukunin mutane da suka gano shi dauke da kayan sana'arsa sun tsayar da shi saboda sunayen da ke rubuce a jikin asusun.
A saman kowani asusun da aka kera da gwangwani akwai sunayen bankunan Najeriya rubuce. An gano Zenith Bank, First Bank, Kuda Bank da sauran manyan bankunan kasar.

Kara karanta wannan
Kada Ku Kashe Ni, Zan Tona Asiri: Matashiya Ta Fashe Da Kuka Yayin da Ta Zauce, Bidiyon Ya Girgiza Jama'a

Asali: TikTok
Asusu dauke da sunayen bankunan ya haddasa cece-kuce
Matasan da ke duba abun da yake siyarwa sun kasa daina dariya yayin da suke kokarin duba sunayen bankunan da suka sani.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Mai tallan ya barsu suna ta dudduba sunayen bankuna daban-daban ganin cewa ya dauki lokacinsa wajen sanyawa kowanne suna da kyau.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
Isabellaosas ta ce:
"Kudi yake nema kasar ta yi wahala."
Prince ya ce:
"Ni ina tunani ko kula ne har sai da na ga uba."
SHU'AEB ADAMS ya tambaya:
"Ina Oopay?"
kev ya ce:
"Ban ga wema bank ba faaa."
Degrace ya yi ba'a:
"Hauka na biya."
Ku shiga ajin koyon dambe a wannan lokacin, Shehu Sani ya shawarci ma'aikatan banki
A wani labari na daban, tsohon sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya shawarci ma'aikatan bankin Najeriya da su yi kokari su shiga ajujuwan koyon dambe a wannan mawuyacin lokaci.
Sani ya ce koyon Judo ko Takwando zai taimaka masu a duk lokacin da fusatattun jama'a suka farmake su a bakin aiki yanzu da ake fama da karancin sabbin kudi a fadin kasar nan.
Yan Najeriya dai suna cikin wani hali na rashin tsabar kudi yayin da masu POS ke cin karensu babu babbaka.
Asali: Legit.ng