Kisan Tsohon Ma'aikacin CBN a Ogun: 'Yan Sanda Sun Samu Babbar Nasara Wurin Bincike
- Rundunar'yan sandan jihar Ogun ta bayyana yadda ta damko wadanda ake zargi da halaka tsohon shugaban Babban Bankin Najeriya, matarsa da 'dansa
- An ruwaito yadda Kehinde Fatinoye, matarsa da 'dansa suka bakunci barzahu a babban birnin jihar Ogun jim kadan bayan dawowarsu daga bikin sabuwar shekara a majami'a
- Sai dai, an bayyana yadda iyalin hatsabiban suka banka wa gidan marigayin wuta, wanda daga bisani aka cafke daya daga cikin wadanda ake zargin, wanda ya kubce daga hannun 'yan sanda
Ogun - Rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta bayyana duk wadanda ake zargi da halaka tsohon ma'aikacin Babban Bankin Najeriya, Kehinde Fatinoye, matarsa da 'dansa a yammacin sabuwar shekara, gami da cafkosu.
Kakakin rundunar 'yan sandan, Oyeyemi Bola ne ya sanar da hakan ranar Talata a wata gajeriyar takarda da ya wallafa a dandalin Twitter.
A cewarsa, Duk wadanda ake zargi da hannu a kisan Fatinoye da matarsa da 'dansa a yammacin sabuwar shekara a Abeokuta sun shiga hannu.
Punch ta ruwaito yadda mummunan lamarin ya auku a yankin Ibara na Abeokuta, babban birnin jihar Ogun da yammacin sabuwar shekara yayin da Kehinde da matarsa Bukola, suka bakunci lahira bayan an konasu kurmus a gidansu na Abeokuta.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An ruwaito yadda makasan suka yi awon gaba da 'dan nasu gami da banka wa gidan wuta.
An tattaro yadda aka yi wa ma'auratan kisan gilla a gidansu na Abeokuta jim kadan bayan dawowarsu daga bikin sabuwar shekara a majami'a.
Daga bisani jami'an 'yan sandan da ma'aikatan lafiyar da suka ziyarci wurin sun tattara gawawwakinsu.
Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya bukaci rundunar 'yan sandan jihar da su bi bayan makasan gami da damkosu.
Sai dai, daga baya an ruwaito yadda aka kama daya daga cikin wadanda ake zargi, wanda ya tsere bayan shiga hannun 'yan sandan a watan Janairu.
Sokoto: 'Yan sanda sun kama wadanda ake zargi da bangar siyasa 10
A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da kamen wasu mutum 10 da ake zargi kan bangar siyasa a jihar Sokoto.
An kama su ne a lunguna da sakonnin jihar daga ciki akwai yankunan Hubbare da Kangiwa Square.
Asali: Legit.ng