'Yan Sanda Sun Damke Matasa da ake Zargin 'yan Bangar Siyasa 10 a Sokoto

'Yan Sanda Sun Damke Matasa da ake Zargin 'yan Bangar Siyasa 10 a Sokoto

  • Rundunar 'yan sandan jihar Sokoto sun kama waus matasa 10 da ake zargi da zama 'yan bangar siyasa a fadin jihar
  • Kwamishinan 'yan sanda ne ya aike jami'ai lunguna da sakonni jihar da suka hada da ofisoshin jam'iyyu har da gidajen fitattun 'yan siyasa
  • An kama su da miyagun makamai, layu da kuma miyagun kwayoyi a ranar Talata da ta gabata a yankunan Hubbare da Kangiwa

Sokoto - Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da kama wasu mutum biyar da ake zargi da zama ‘yan daban siyasa da suka addabi yankuna daban-daban a jihar, jaridar Punch ta rahoto.

'Yan daba
'Yan Sanda Sun Damke Matasa da ake Zargin 'yan Bangar Siyasa 10 a Sokoto. Hoto daga Punchng.com
Asali: UGC

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Sanusi Abubakar, wanda ya tabbatar da cigaban a wata takarda a ranar Talata, yace makamai, layu da miyagun kwayoyi aka samu daga wadanda ake zargin.

Kara karanta wannan

Hotuna: Yadda Tinubu ya Ziyarci Mahaifiyar Marigayi ‘Yar’adua a Katsina

Jaridar Tribune Online ta rahoto cewa, Abubakar yace wannan cigaban an same shi ne sakamakon umarnin da kwamishinan ‘yan sanda, Mohammed Gumel, ga kwamandoji da DPO da suka kai samame yankunan da ke da ‘yan daba balle ofisoshin kamfen da gidajen ‘yan siyasa kuma su tabbatar da cewa babu wurinsu a jihar.

Takardar tace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Yan sandan tare da hadin guiwar jami’an wasu hukumomi tsaro kan zabe sun kawo matakan hana tashin-tashina inda suka kama 'yan daban siyasa 10 da miyagun makamai, layu da kwayoyi a yankuna daban-daban na jihar.
"A sakamakon duba ababen hawan da ake yi, 'yan sanda sun kama 'yan daba a Kangiwa Square yayin da sauran aka kama su a yankin Hubbare.
"A yayin rubuta wannan rahoton, dukkan wadanda ake zargin an gurfanar da su gaban kotu kuma an aike su gidan gyaran hali a Sokoto."

Kara karanta wannan

‘Yan Daban Siyasa Sun Kai Hari Ana Taron Jam’iyyar PDP, An Raunata Mata da Matasa

Yayin bayyana cewa za a cigaba da farautar 'yan daban, Abubakar yace Gumel ya umarci dukkan DPO da su cigaba da duba ofisoshin kamfen, jam'iyyu tare da gidajen 'yan siyasa da ke da dabi'ar tara 'yan daba.

EFCC sun damke manajan banki da ya boye N29 miliyan a ma'adanar kudinsu

A wani labari na daban, jami'an hukumar EFCC sun cafke manajan bankin 'yan kasuwa a ABuja bayan sun samu kudi har N29 miliyan a ma'adanarsu.

Jama'a sun sha layi sannan wasu suna ATM amma ba a zuba kudin ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel