Hankula Sun Tashi Yayin Da Yan Bindiga Suka Kashe Sojoji 4 A Harin Kwanton Bauna A Delta
- Wasu bata gari da ba a san ko su wanene ba sun afka wa dakarun sojojin Najeriya a garin Kwale da ke karamar hukumar Ndokwa West ta Jihar Delta
- A yayin harin kwanton baunar, maharan sun bindige sojoji uku har lahira nan take sannan wani sojan daga basani ya rasu bayan an kai shi asibiti
- A halin yanzu ana zaman dar-dar a garin na Kwale yayin da aka ce dakarun sojoji sun bazama cikin garin da nufin binciko maharan
Jihar Delta - Rahotanni da suka fitowa sun nuna cewa yan bindiga sun kai wa dakarun sojojin Najeriya hari a Kwale, karamar hukumar Ndokwa West na Jihar Delta.
The Punch ta rahoto cewa sojoji hudu sun rasa ransa sakamakon harin.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Lamarin da ya faru a ranar Alhamis ya haifar da tashin hankali a hanyar Kwale yayin da aka ce jami'an sojoji sun kutsa garin.
Majiya ta magantu kan yadda harin da aka kai wa sojoji a Kwale ya faru
Wani majiya daga garin ya fada wa Punch cewa bata garin sun yi wa sojojin kwanton bauna ne suka kashe uku nan take.
Saura kuma sun samu mabanbantan rauni inda aka garzaya da su Cibiyar Lafiya na Tarayya, FMC, da ke Asaba.
Ya ce:
"Bata garin sun yi wa sojojin kwanton bauna suka kashe uku cikinsu nan take, an garzaya da saura Cibiyar Lafiya na Tarayya da ke Asaba.
"Daya daga cikin sojojin ya mutu a FMC saboda ya rasa jini sosai a jikinsa."
Kawo yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar yan sanda ko sojoji a jihar ta Delta.
Yan bindiga sun sheke farar hula 68 da dakarun sojoji 10 a Zamfara
A wani rahoton, kun ji cewa kimanin sojoji 10 ne da farar hula guda 68 suka riga mu gidan gaskiya sakamakon wani mummunan hari da yan fashin daji suka kai garin Mutunji da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara, ranar 18 ga watan Disamba.
Rahotanni sun bayyana cewa an dauki gawarwakin jami'an tsaron da suka riga mu gidan gaskiya an kai su Asibitin Kwararru na Yariman Bakura da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
Maharan sun afka wa sojojin da ke atisayen tabbatar da zaman lafiya a yankin ne yayin da suke hanyarsu na zuwa garin Mutunji.
Asali: Legit.ng