Gangamin Yaƙin Neman Zaɓe: Yadda Peter Obi Ya 'Fusata' Magoya Bayansa Jihar Yobe

Gangamin Yaƙin Neman Zaɓe: Yadda Peter Obi Ya 'Fusata' Magoya Bayansa Jihar Yobe

  • Magoya bayan jam'iyyar Labour wato LP a jihar Yobe sun 'fusata' sakamakon jira da suka yi amma Peter Obi bai zo ba
  • An shirya yin kamfen din Obi na jihar ta Yobe ne a ranar Talata 7 ga watan Fabrairu amma hakan bai yi wu ba duk da magoya baya sun sha jira a filin jirgin sama
  • Hauwa Bukar, shugaban kamfen din Obi-Datti na Arewa maso Gabas ta bawa magoya bayan jam'iyyar hakuri, tana mai cewa hukuma ba ta bada izinin sauka a filin jirgin sama na Yobe bane

Jihar Yobe - A ranar Talata 7 ga watan Fabrairu, Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, ya bata wa magoya bayan sa a Damaturu, babban birnin jihar Yobe, rahoton Daily Trust.

An sa ran Obi da abokin takararsa Dr Datti Baba Ahmed, za su ziyarci jihar ne domin kamfen din takarar shugaban kasa, wacce aka yi shirin yi a dakin taro na Conference Hotel a Damaturu misalin karfe 11 na safe.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Babu Wani Dan Najeriya Mai Hankali Da Zai Zabi APC Ko PDP A 2023

Obi Datti
Gangamin Yakin Neman Zabe: Peter Obi Ya 'Bata Wa Magoya Bayansa Rai' A Yobe. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yan takarar da jam'iyyar Labour da magoya bayansu sun yi ta jiran zuwan Obi a filin tashin jiragen sama na Muhammadu Buhari da ke Damaturu, amma bai taho ba.

Hakan ya harzuka wasu daga cikin magoya bayan inda suka bukaci shugabannin jam'iyyar su basu kudin cin abinci kamar yadda aka musu alkawari tunda farko.

Wasu daga cikin su sun bayyana abin da Obi ya yi a matsayin ragwanci.

Ba da gangan Obi ya ki zuwa kamfen Yobe ba, Hauwa Bukar

Da ta ke jawabi ga magoya bayan jam'iyyar, Hajiya Hauwa Bukar, jagoran kwamitin kamfen din Obi-Datti na Arewa maso Gabas ta roki a yafe musu, tana mai cewa ba da gangan bane.

Ta ce hukumomin da hakkin ya rataya a kansu ba su bada izini jirgin Obi ya sauka a filin jirgin ba.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Allah Na Dogara Da Shi Domin Nasara," Tinubu Ya Fada Wa Mahalarta Taron Ruwa Da Tsaki Na APC

Bukar ta ce kawo yanzu gwamnatin tarayya ba ta riga ta kaddamar da filin sauka da tashin jiragen ba.

Ta kara da cewa za a sake zaben wani sabon rana da Obi zai taho kamfen a jihar na Yobe.

Zaben 2023: Ku Karbi Kudinsu Idan Sun Baku Amma Ku Zabe Ni, Peter Obi Ya Fada Wa Magoya Bayansa

A wani rahoton da muka kawo kun ji cewa dan takarar na shugaban kasa na LP, Peter Obi, ya fada wa magoya bayansa su amshi kudi daga APC da PDP amma kadu su zabe su.

Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya fada wa magoya bayansa a Ilorin, Jihar Kwara cewa dama kudin nasu ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel