Sauya Naira: Dalilinmu Na Kai Gwamnati, CBN Zuwa Kotu - El Rufai Ya Saki Jawabi

Sauya Naira: Dalilinmu Na Kai Gwamnati, CBN Zuwa Kotu - El Rufai Ya Saki Jawabi

  • Malam Nasir El-Rufai ya yabi kotun koli a kan hukuncin da aka zartar da ya takawa CBN burki
  • Gwamnatin jihar Kaduna ta ce bankin CBN ya jefa al’umma a kunci a yunkurin canza Nairori
  • A jawabin murnar da ya fitar, El-Rufai ya nuna halin da aka shiga ne ya jawo suka kai batun kotu

Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna tayi farin ciki da hukuncin da kotun koli ta zartar a game da batun hana amfani da tsofaffin Naira a fadin Najeriya.

A wata sanarwa da Mai taimakawa Gwamnan Kaduna wajen yada labarai da sadarwa ya fitar a Twitter, ya yi maraba da nasarar da suka samu.

Da yake magana a a ranar Laraba, Muyiwa Adekeye ya ce jihar Kaduna da miliyoyin mutanenta sun ji dadi da jin cewa kotu ta dakatar da wa’adin CBN.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Wike Ya Magantu Kan Hukuncin Kotun Koli, Ya Faɗi Matakin Da Zai Dauka Kan Sabbin Kuɗi

Gwamnatin Nasir El-Rufai ta soki wannan tsari na bankin CBN da cewa an yi garaje, bai zo lokacin da ya dace ba, sannan ba ayi cikakken nazari ba.

Nasir El-Rufai ya jinjinawa kotun koli

Kamar yadda aka bayyana a wannan jawabi, Mai girma Nasir El-Rufai ya yabawa Alkalan kotun koli da jami’an gwamnati da suka taimaka wajen karar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Malam El-Rufai yake cewa gwamnatocin Kaduna, Zamfara da Kogi sun ga cewa dole a tunkari kotu domin a fitar da mutane daga wahalar da aka jefa su.

El Rufai
Gwamnan Kaduna a Aso Rock Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Gwamnan na Kaduna ya ce babu dalilin da zai sa a hana mutane damar rike dukiyarsu.

Mun zauna da Hukuma - El-Rufai

Mista Muyiwa Adekeye yake cewa gwamnoni sun zauna da gwamnatin tarayya da bankin CBN, suka gabatar masu da hujjojin barnar sauya kudi a yanzu.

Gwamnatin Kaduna ta na ikirarin tsarin ba zai amfanar da tattalin azikin kasa da talakawa ba.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Buhari na ganawar sirri da gwamnan CBN bayan hukuncin kotun koli kan batun kudi

A karshen jawabin, Gwamnan ya ce yana fata za ayi wa tsarin canjin kudin kwaskwarima ta yadda za a samu isassun tsofaffin da sababbin Naira.

Kamar yadda sauran Gwamnonin APC masu-ci suka bada shawara, El-Rufai ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta bi tsarin yadda ake yi a inda aka cigaba.

CBN ne barazanarmu - Bamidele

An rahoto Sanatan Ekiti ta tsakiya, Michael Opeyemi Bamidele ya ce tsarin CBN yana da tasiri a harkar siyasar tattalin arzikin ga sha’anin zabe mai zuwa.

Michael Bamidele ya ce Hukumar INEC ba za ta iya yin aikinta ba saboda tsarin bankin CBN. ‘Dan majalisar ya zargi CBN da zama babban ala-ka-kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng