Kada Ku Kai Tsaffin Kudinku Banki, Tinubu Na Hawa Mulki Zai Yi Watsi da Dokar: El-Rufa'i

Kada Ku Kai Tsaffin Kudinku Banki, Tinubu Na Hawa Mulki Zai Yi Watsi da Dokar: El-Rufa'i

  • Gwamna Nasir El-Rufa'u ya yiwa al'ummar jiharsa alkawarin cewa babu abinda zai sami tsaffin kudinsu
  • El-Ru'fai ya ce mutan jihar su cigaba da harkokinsu da tsaffi da sabbin kudi kuma sako ne da Tinubu
  • Ya ce duk wanda ke da tsaffin kudi ya kawo gidan gwamnati zasu karba kuma dole bankin CBN ya karba

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya bayyanawa yan kasuwar jiharsa su cigaba da amfani da tsaffin kudadensu kuma ya basu tabbacin babu abinda zai faru.

A wani taro da yan kasuwa ranar Talata, El-Rufa'i ya ce idan aka zabi Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, matsayin shugaban kasa, zai yi watsi da dokar sauya fasalin Naira.

El Rufa'u
Kada Ku Kai Tsaffin Kudinku Banki, Tinubu Na Hawa Mulki Zai Yi Watsi da Dokar: El-Rufa'i
Asali: Facebook

El-Rufa'i ya baiwa yan kasuwan tabbacin cewa duk wanda ya rasa kudinsa ya kamasu da alhaki amma yana musu alkawarin babu abinda zai samu kudinsi.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya sun koma kwana gindin ATM saboda tsananin rashin kudi

Yace:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ku daina canza kudadenku kuma ku fadawa kowa ya daina kai kudinsa banku. Idan sun sayar da wani abu, ku ajiye tsaffin kudadenku. Ku daina cewa sabbin kudi kadai zaku karba saboda kasuwancinku zai tsaya kuma haka suke so."
"Ku fadawa kowa a Kaduna mai tsaffin kudi su kashe kudinsu. Ku fadawa kowani dan kasuwa ya kashe kudinsa."
“Nasir el-Rufai, Uba Sani, da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na muku alkawarin cewa idan aka zabemu, za'a canza wannan doka kuma kowa zai samu isasshen lokaci don sauya kudinsa."

Kalli jawabinsa:

Ku canza hukuncinku na lamarin tsaffin Naira, gwamnati ta bukaci kotun koli

Gwamnatin tarayya ta yi kira ga kotun kolin Najeriya tayi watsi da karar da gwamnonin APC suka shiga ne bukatar soke ranar 10 ga Febrairu, 2023 matsayin ranar karshe na daina amfani da tsaffin takardun Naira.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum Ya Bi Banki-Banki Yana Musu Barazanar Kullesu Idan Basu Fito Da Kudi Ba

Gwamnonin da suka shigar da kara sune gwamnan jihar Nasir El-Rufa'i, Gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.

Gwamnonin su uku gabatar da bukata gaban kotun koli na a hana da shirin haramta amfani da tsaffin takardun Naira na N1000, N500 da N200 da gwamnatin tarayya da babban bankin tarayya CBN ke kokarin yi a ranar 10 ga Febrairu, 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel