Gwamna Zulum Ya Bi Banki-Banki Yana Musu Barazanar Kullesu Idan Basu Fito Da Kudi Ba

Gwamna Zulum Ya Bi Banki-Banki Yana Musu Barazanar Kullesu Idan Basu Fito Da Kudi Ba

  • Har yanzu yan Najeriya na cigaba da fama da matsalar karancin tsabar kudi, tsaffi ko sabbin ma
  • Gwamna Zulum ya fusata ya bi rana bankunan dake birnn Maiduguri yana jan kunne ga manajojin bankunan
  • A kudancin Najeriya, fusatattun matasa sun yi kone-konen bankuna da tayoyi cikin zanga-zanga

Maiduguri - Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bi banki-banki a cikin birnin Maiduguri yana musu gargadi kan rashin baiwa jama'a sabbin kudade.

Zulum ya yi barazanar cewa duk bankin da suka ki fito da kudi wa mutane za'a kwace hakkin filin da bankin ke zaune kuma a rufe bankin kai tsaye.

Gwamnan yace uzurin da zai musu shine kawai idan CBN bata basu isasshen kudi ba.

Zulum
Gwamna Zulum Ya Bi Banki-Banki Yana Musu Barazanar Kullesu Idan Basu Fito Da Kudi Ba Hoto: @GovBorno
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Naira: El-Rufa'i Da Yahya Bello Sun Dira Kotun Koli Inda Za'a Yanke Hukunci Yanzu

Zulum ya bada wannan umurni ne ranar Juma'a a Maiduguri bayan ziyartar bankunan kan wahalar da mazauna jihar ke fuskanta wajen samun kudi.

Yace:

"Duk wani banki a Borno da bai da niyyar tabbatar da cewa na'urarsu ATM na fitar da isassun kudi don saukaka rayuwar al'ummarmu, zamu janye hakkin filinsu kai tsaye. Bankunan da ke da wani uzuri kadai zamu bari."
"Kamar yadda kuke gani, talakawa ke layi a nan. Ban ga attajirai a nan ba. Wasu tun karfe 3 na dare suke nan, wasu ko abinci basu ci ba. Sabbin kudin da tsaffin kudi, duk babu kuma hakan na illata kasuwancin mutan jihar kuma suna wahala."

" Kwanan muka biya albshi N5bn kuma bankuna na cewa basu da kudi, wasu ATM ba su aiki."

"Yanzun nan a Borno na duba wasu ATM sama da 10 kuma babu kudi."

Sauya Fasalin Naira Ya Rage Laifin Garkuwa da Mutane da Kuma Rashawa, Malami

Kara karanta wannan

Bankuna sun turawa kwastomomi sabon sako mai muhimmanci game da karancin kudi

A wani labarin kuwa, Antoni Janar na tarayya kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, yace sauya fasalin Naira da babban bankin Najeriya CBN tayi ya rage matsalar garkuwa da mutane a kasa.

Malami, a wata hira da yayi a gidan Radio Nigeria Kaduna, tace akwai alkhairai da babu wanda ke magana a kai, rahoton DailyTrust.

A cewarsa: "Na fada muku lamarin na kotu, zamu bi umurnin kotun amma muna da hakknin yiwa kotun bayanin amfanin wannan tsari."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel