Sabuwar Na'urar Da Za'a yi Amfani a Zaben 2023: Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Ita
- Gabanin babban zaben 2023, an bukaci masu zabe su yi kokarin sanin sahihan bayanai kafin zuwa wurin zaben
- A watannin da suka gabata, INEC na cigaba da wayar da kan mutane tare da hadin gwiwar kungiyoyin tallafawa al'umma don fadar da mutane
- Daya cikin muhimman bayanan da INEC ke fadakarwa shine yadda na'urar Bimodal Voter Accreditation System (BVAS) ke aiki
Kasa da sati biyu kafin babban zaben 2023, masu zabe sun kosa su tafi su sauke nauyin da doka ta dora musu na zaben yan takarar da suke so.
Amma, zaben na 2023 ya taho da wasu canje-canje da wasu ababen da suka sa zaben wannan shekarar ya banbanta da saura.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daya cikin sabbin ababen da aka kawo a tsarin zaben Najeriya shine tsarin Bimodal Voter Accreditation System (BVAS).
INEC ta gabatar da BVAS ne a shekarar 2021 don inganta nagartar zabe da dakile magudi, don haka ya maye gurbin smart card reader.
Muhimman abubuwa biyar game da BVAS da yadda ya ke aiki
1. BVAS din zai karanta bayannai da ke PVC ya tantance bayanan mai zaben (zaben yatsu da fuska) kafin zabe.
2. Don karanta PVC, na'urar zai haska barcode ko QR da ke PVC ko rajistan masu zabe. Jami'in zabe kuma zai iya shigar da lambobi shida na karshe na lambar katin zabe wato VIN ko sunan karshe da ke katin zabe don tantance masu zabe.
3. Bayan tantancewa, za a yi amfani da BVAS don dora sakamakon zabe daga rumfunan zabe zuwa matattaran bayanai na INEC a yayin da ake yin zaben.
4. Don yin hakan, BVAS zai dauki sakamakon zabe daga rumfunan zabe kuma nan take ya tura zuwa matattaran bayanai da al'umma ke iya gani.
5. BVAS baya bukatar sabis na intanet domin yin aiki. Idan har an saita na'urar daidai kuma an yi cajin batirinsa, zai iya aiki ba tare da matsala ba. Ana bukatar intanet ne kawai yayin tura sakamakon zabe.
INEC: Ba mu tunanin dagewa ko soke babban zaben shekarar 2023
A bangare guda, hukumar zabe mai zaman kanta na INEC ta yi magana dangane da yiwuwar dage babban zaben 2023.
Farfesa Mahmud Yakubu, shugaban hukumar na kasa ya ce ba ya tunanin dagewa ko soke zaben.
Asali: Legit.ng