Bidiyon Yadda ’Yan Najeriya Ke Girki a Cikin Banki Yayin Jiran Layin Karbar Sabbin Naira

Bidiyon Yadda ’Yan Najeriya Ke Girki a Cikin Banki Yayin Jiran Layin Karbar Sabbin Naira

  • Mutanen garin Aba sun ce ba za su bar cikinsu da yunwa ba yayin da suke jiran a basu sannin Naira a layin ATM
  • An ga mutanen a zaune a bakin banki kusa da injin ATM suna girka taliya yayin da suke jira layinsu ya iso
  • Bidiyon da Legit.ng ta samo ya nuna cewa, tabbas a wurin mutanen suka girka abincinsu don gujewa yankan kayi

Yayin da ake ciki gaba da layin neman sabbin Naira a Najeriya, mutane suna ta gano hanyoyin da za su rayu ba tare da wata matsala ba a kusa da banki.

Yayin da wasu ke ta zanga-zanga a garuruwan irinsu Oyo, wasu mazauna Aba a Najeriya sun mai da bakin banki wurin cin abinci.

A bakin bankin, an ga mutanen yankin sun zo da gas din girki, tukwane da sauran abubuwan girki a matsayin tanadi.

Kara karanta wannan

Albishir ga 'yan Najeriya: NNPC ya fadi lokacin da fetur zai wadata, ya yi alkawari daya

A wani bidiyon da Legit.ng ta samo an yada a kafar sada zumunta ya nuna lokacin da mazauna Aba ke jiran layin cire kudi a ATM, kana suna girka abin da za su saka a ciki.

An koma dafa abinci a banki saboda layin ATM
Bidiyon Yadda ’Yan Najeriya Ke Girki a Cikin Banki Yayin Jiran Layin Karbar Sabbin Naira | Hoto: @Ehijiiie, Bashir Ahmad
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wani yankin bidiyon, an ga wasu maza hudu ya cin taliya daga tukunya kafin a sauke a daidai lokacin da suke kan layin ATM.

Cin taliya ba kakkautawa a bakin banki

Matasan dai sun dukufa sai cin abincinsu suke, wasu mutane da ke kan layi kuwa sai kallonsu suka cikin mamaki.

Wata murya da ke cikin bidiyon ta bayyana cewa, mutanen sun shafe awanni a bakin bankin don cire kudi amma basu samu ba, sun kuma ki hakura da bin layi.

Muryar, (Da harshen Igbo) ta ce, sun jira layin ne na tsawon lokaci ta yadda dole su jira don cire kudin, don haka suka yanke shawarin yin girki.

Kara karanta wannan

Karancin sabbin Naira: Kwastomomi na ta kuka, bankuna sun rufe kofofinsu da safe

Kalli bidiyon:

An kama manajojin banki suna boye sabbin kudi

A wani labarin kuma, kun ji yadda jami’an hukumar ICPC suka kwamushe wasu manajojin bankin Sterling a babban birnin tarayya Abuja.

An kuma bankado wasu manyan kudade; N258m da aka boye a ma’ajiyar banki yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da layin neman sabbin kudi a kasar.

A wannan karon, babu abin da ‘yan Najeriya suka fi jin zafinsa kamar karancin sabbin Naira a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.