Wata Mata Ta Sharbi Kuka, Ta Ba Dillali N1.2m Ya Samo Mata Gidan Haya, Ya Hada Ta da Jagwal

Wata Mata Ta Sharbi Kuka, Ta Ba Dillali N1.2m Ya Samo Mata Gidan Haya, Ya Hada Ta da Jagwal

  • Wani bidiyon mata ‘yar Najeriya da ta biya kudin haya N1.2m ga dillali don kama gida ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta
  • Ba tare da ganin gidan ba, an ce matar ta ba da kudi N1.2m, amma da ganin gida hankalinta ya tashi, ta ga sabanin abin da take tsammani
  • Abin bakin ciki, da ta ga gidan babu yadda yake, sai kawai ta barke da kuka, ta bayyana bacin ranta da abin da aka mata

Wata mata ‘yar Najeriya ta shiga jimami da kwaranyar hawaye yayin da ta ga gidan ta ba da N1.2m aka ba ta haya.

A bidiyon da ta yada, an ga tana sharbar kuka yayin da dillali ya kai ta ganin gidan da ta ba da kudi ya kama mata.

Ta bayyana cewa, ta aminta da dillalin har ta kai ga ba shi kudadenta don sama mata matsuguni, bata san na kasa na kasa ba.

Kara karanta wannan

A ina kika samo: Kowa girgiza, wata mata ta samo damin kudi, tana siyar da N50k a farashin N60k

Mata 'yar TikTok ta ba da labarin yadda ta sha wahala a hannun dillali
Wata Mata Ta Sharbi Kuka, Ta Ba Dillali N1.2m Ya Samo Mata Gidan Haya, Ya Hada Ta da Jagwal | Hoto: @maryvin2324
Asali: TikTok

Abin bakin ciki, dillalin ya samo mata wani balkwataccen gida da bata yi tsammani ba, hakan ya kada tunaninta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A bidiyon da ta yadu a TikTok, an ga matar na sharbar kuka yayin da take zagayawa a cikin gida, kama daga katanga har dakuna duk a birkice suke.

Da ta yada bidiyon, ta ce:

“Bayan ba dillali N1.2m domin sama min gida, kalli abin da ya samo min."

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a

@sodick_gh1:

"Kin fi kowa rashin hankali ne. Ta yaya za ki biya kafin kiga abin da za siya

@steven00332:

"Baki da kai ne tunda kika ba dillali kudi don nema miki bukka.”

@blesstiktoker:

"Kenan baki duba gidan ba kafin ki ba da kudi ko kuma yaya ne.”

@prosperprosper326k:

"Ta yaya mutum mai hankali zai biya kudin hayan gida ba tare da ganinsa ba. Wannan ba hauka bane.

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Ta yi aure a shekaru 50, ta haihu a shekara 71, bidiyon tsohuwa ya ba da mamaki

@peaceworld50:

"Meye yasa za ki biya kudin abin da baki gani a Najeriya, sai hakuri.”

@uche_china:

"Ta yaya za ki biya kudin abin da baki gani ba kuma kina tunanin za ki ga abu mai kyau daga fuskar wadannan yaran.”

Tsadar kudin haya na daya daga cikin abubuwan da ke ba 'yan Najeriya wahala; musamman a jihar Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel