Kotu Ta Wanke 'Dan Gwamnan Bauchi Daga Zargin Badakalar N1.1bn

Kotu Ta Wanke 'Dan Gwamnan Bauchi Daga Zargin Badakalar N1.1bn

  • Hukumar yaki da rashawa, EFCC, ta samu koma baya kan zargin rashawar da take yiwa 'dan gwamnan Bauchi
  • Alkalin kotu ya ce hukumar yaki da rashawan ta gaza tabbatar da gaskiyar zargin da take yiwa 'dan gidan gwamnan
  • Mahaifin Shamsidden na neman zarcewa kan kujerar gwamnan jihar Bauchi a zaben Maris, 2023

Abuja - Wata babban kotun tarayya dake zamanta a Abuja ta wanke Shamsudden Bala, 'dan gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, daga zargin almundahanar N1.1 billion.

A hukuncin da aka yanke ranar Talata, Alkali Nnamdi Dimgba ya bayyana cewa EFCC ta gaza gabatar da isassun hujjojin kamar yadda doka ya bukata.

Shamsuddeen ya bayyanawa Alkali cewa yana cikin dimuwa ne lokacin da ya fadawa EFCC cewa lallai gaskiya da zargin da ake masa, rahoton TheNation.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Shugaban INEC Ya Sa Labule Da Gwamnan CBN Saboda Karancin Takardun Naira

Alkalin ya amince da wannan uzuri kuma ya ce asusun bankin da EFCC ke zargin yana boye kudi ba ya karkashin kulawarsa, matarsa ke juya kudin.

kaura
Kotu Ta Wanke 'Dan Gwamnan Bauchi Kan Zargin Badakalar N1.1bn
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace:

"Asusun banki bai karkashin kulawarsa (Bala), yana karkashin kulawar matarsa."
"Masu kara sun gudanar da bincike kan ikirarin wanda ake zargi na cewa cikin dimuwa da firgici ya cika Fam da dukiyoyin da ya mallaka."
"Masu kara ne kadai zasu iya bincike a ilmanci kan halin da wanda ake zargin ke ciki lokacin da suka damke shi."

A baya Alkali Dimga ya soke tuhuma 11 cikin 20 da EFCC ke yiwa Shamsudden Bala Mohammed.

Zargin da EFCC ke masa

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC ya shigar da Shamsudden Bala tare da kamfanoni 4 kotu bisa almundahanar dukiyoyi.

Kara karanta wannan

Gwamnan CBN Karya Kawai Ya Shararawa Shugaba Buhari: Babban Hadimin Shugaban Kasa

Kamfanonin sun hada da Bird Trust Agro Allied Ltd, Intertrans Global Logistics Ltd, Diakin Telecommunications Ltd da Bal-Vac Mining Ltd.

EFCC ta ce Shamsudden Bala ya yi amfani da wadannan kamfanoni ne wajen almundahanar kudi N1.1bn.

Ta ce Bala ya sayi gidaje masu tsada a Abuja da kudi Lakadan, kudi a hannu.

Hukumar ta ce wasu daga cikin dukiyoyin da ya saya sune fulotin filaye biyar a Asokoro Gardens; Gida mai lamba FD 2B a Green Acre Estate Apo Dutse; Gida mai lamba FS 1A a Green Acre Estate Apo Dutse; Gida mai lamba FS 1B a Green Acre Estate Apo Dutse; da gida mai lamba 7, Gana Street, Maitama Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel