Bidiyon Yadda Wata Ke Siyar da Sabbin Naira Ga Attajirai Ya Tada Kura a Twitter
- ‘Yan Najeriya sun dauki dumi a shafin Twitter yayin da aka ga wata mata na tallan sabbin kudi a bainar jama’a a wani gari
- An sauya fasalin Naira a Najeriya, ‘yan Najeriya na ci gaba da fuskantar karancin sabbin kudi, suna dogon layi a banki
- Gwamnatin Najeriya ta ce za ta tabbatar da kawo mafita ga matsalar kudi nan ba da jimawa ba, ta bayyana ta yaya hakan zai faru
Najeriya - Wani bidiyon da ya yadu a Twitter ya nuna lokacin da wata mata ke siyar da sabbin Naira ga wasu mutane a jikin manyan motoci.
An ji muryar wani mutum da ke neman a bashi N50,000, inda ya ambaci zai tura N60,000 don samun sabbin Naira na N50,000.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke fama da karancin sabbin Naira a bankuna da hannun agent-agent da ke musayar kudade a kasar.
A bidiyon, an ji lokacin da wani mutum ke tambayar matar a ina take samo kudaden, inda tace tana samo su ne daga banki, wurin manaja.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Laifin Emefiele ne, inji wanda ya yada bidiyon
DeeOneAyekooto da ya yada bidiyon a Twitter, ya ta’allaka laifin siyar da kudin ga gwamnatin CBN Godwin Emefiele, tare da cewa wannan abin kunya ne ga gwamnan.
Jama’ar kafar sada zumunta sun shiga mamakin yadda wasu ke samo kudaden daga bankuna, wasu kuma ke shan fama da rashin sabbin kudin.
Tun bayan sauya N200, N500 da N1000 ake fama da matsalar karancin sabbin kudi, an sha kama manajojin banki da laifin boye kudaden a ma’ajiyar banki.
Kalli bidiyon:
Martanin jama’a
@Skino4u:
“Kun ji kunya manajojin banki.”
@kemiwarrior:
“Laifin mutanen da ke siya ne.
“Kamata ya yi su mika matar ga ofishin ICPC/EFCC mafi kusa.”
@fadysocial:
“Meye dalilin ganin laifin Emefiele a nan? Za ka iya nuna min wani shiri na gwamnati da ‘yan Najeriya suka bari ya yi aiki ba tare da wata matsala ba a baya?”
@fatlaro:
“Ku ga laifin manajojin banki da ma’aikatansu.”
@EjiykeP:
“Ku tuhumi manajojin bankunanku marasa tausayi ba CBN ba.”
@RexTokus:
“Ta haka muke ganin laifin wasu da bai shafe su ba muke kuma ba wasu lambar yabo duk da su ne makiyan kasa.”
Buhari ya ce zai tabbatar da kowa ya samu sabbin Naira, kuma kudi za su wadata a fadin kasar nan da kwanaki bakwai, lamarin da wani sanata ya kalubalanta.
Asali: Legit.ng