Ku Cigaba da Bin Layi Ba Zamu Kara Wa'adin Naira Ba Bayan Ranar 10 ga Febrairu, Gwamnan CBN

Ku Cigaba da Bin Layi Ba Zamu Kara Wa'adin Naira Ba Bayan Ranar 10 ga Febrairu, Gwamnan CBN

  • A watan Diamba 2022 gwamnatin shugaba Buhari ta sanar da cewa za'a sauya fasalin takadun Naira
  • Takardun Kudin da wannan sauyi ya shafa sune N1000, N500 da N200, daga baya aka ce a cigaba da amfani da N200
  • Yan Najeriya da dama sun bayyana irin halin da suka shiga sakamakon wannan sauyi na kudi

Abuja - Gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa ba zasu sake daga ranar karse na daina amfani da tsaffin takardun Naira ba.

Emefiele ya bayyana hakan ranar Juma'a yayin hira da manema labarai a ofishin bankin dake jihar Legas.

Ya bayyana cewa suna iyakan kokarinsu domin magance matsalar karancin sabbin takardun kudin da jama'a ke fama da shi.

A cewarsa:

"Ina son in kara fada muku cewa wannan karon gaskiya ba mu tunanin dage wa'adin saboda mu a babban banki da kuma sauran bakuna muna iyakan kokarin don magance matsalan."

Kara karanta wannan

Shin Tsoffin N500 da N1000 Zasu Ci Gaba da Amfani Bayan Hukuncin Kotun Koli? Sabbin Bayanai Sun Fito

Ya yi kira ga yan Najeriya su cigaba da bin layi kuma suyi hakuri saboda amfanin sauyin fasalin Nairan ya rinjayi wahalar da suke sha.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Naira
Ku Cigaba da Bin Layi Ba Zamu Kara Wa'adin Naira Ba Bayan Ranar 10 ga Febrairu, Gwamnan CBN
Asali: Getty Images

Ya mayar da martani ga gwamnan Kano da sauran masu cewa yana da wata manufa ta musamman.

Ya ce musu manufarsa daya ce kuma itace gyara tattalin arzikin Najeriya.

A cewarsa:

"Aikinmu mukeyi. Mu ma'aikatan banki ne. Masu zanga-zanga kada su bari wasu su yi amfani da su."

Asali: Legit.ng

Online view pixel