Gwamna Abiodun Ya Mamaye Banki, Ya Nemi a Saki Sabbin Kuɗi Ga Jama'a

Gwamna Abiodun Ya Mamaye Banki, Ya Nemi a Saki Sabbin Kuɗi Ga Jama'a

  • Gwamnan jihar Ogun ya mamayi reshen CBN da ke Abeokuta domin duba abinda ya sa sabbin takardun naira suke ƙaranci
  • Dapo Abiodun ya dauki wasu kwararan matakai da zasu taimaka wajen ragewa talakawa radaɗin wahalar
  • Yace baya jin daɗin yadda mutane ke kwana a layin ATM amma daga karshe a basu naira dubu biyu kacal

Ogun - Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya ziyarci reshen babban bankin Najeriya (CBN) da ke Abeokuta, ranar Litinin kan karancin takardun sabbin naira.

Gwamnan ya kuma tattauna da ma'aikatan reshen CBN ɗin game da ƙaruwar wahalar rayuwa wacce al'umma suka wayi gari a ciki sanadin canja takardun naira.

Karancin sabon kuɗi a Ogun.
Gwamna Abiodun Ga Mamaye Banki, Ya Nemi a Saki Sabbin Kuɗi Ga Jama'a Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Abiodun tare da rakiyar shugaban majalisar dokokin Ogun, Olakunle Oluomo, da wasu kusoshin gwamnatin jihar sun kai ziyarar bazata reshen CBN na jihar, kamar yadda Dailytrust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: Abinda Ya Faru da Wani Sarki Mai Martaba Lokacin da Ya Je Banki Neman Sabbin Kuɗi

Gwamnan ya kuma gana da kungiyar bankunan, wacce ta kunshi Manajojin bankunan kasuwanci masu zama a sassan jihar Ogun.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wane mataki ya ɗauka domin saukakawa jama'a?

Gwamna Abiodun ya umarci CBN reshen jiharsa da kuma shugabannin bankunan kasuwanci su tabbata sun samarwa al'umma sabbin takardun naira da zasu cire.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa Dapo Abiodun ya yi haka ne domin talakawa su samu saukin wahala da layukan da suke fama yayin jiran a sa kuɗi a ATM su cire.

Haka zalika ya yi tayin jagorantar mambobin majalisar zartarwansa domin sa ido kan yadda CBN ke rabawa bankunan kasuwanci sabbin takardun N200, N500 da kuma N1000.

Bugu da kari zai ƙara kaimi wajen sa ido da nufin tabbatar da cewa Bankunan kasuwanci da kuma wakilansu ba su karkatar ko boye sabbin kuɗin da suka karbo ba

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Irin barnar da fusatattun matasa suka yi Banki a Ibadan

A cewarsa, abun da takaici yadda mutane ke haɗa uban layi a ATM suna jiran cire sabbin kuɗi cikin wahala kuma ba dan komai ba sai don aiwatar da bukatun rayuwa na yau da kullum.

Ya ƙara da cewa abun kunya ne waɗannan mutane duk wahalar da suka sha Naira dubu biyu kacal zasu samu ikon cirewa, rahoton Punch ya tabbatar.

A wani labarin kuma mun zaƙulo muku gaskiya game da ainihin ranar daina amfani da tsaffin kuɗi tsakanin 10 da 1ƴ ga wata da kuma wasu bayanai masu muhimmanci.

Idam baku manta ba gwamnan CBN ya bayyana cewa bankin zai ci gaba da karban tsofaffin takardun naira har bayan ƙarewar wa'adin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel