Jam'iyyun SIyasa 13 a Najeriya na Barazanar Kauracewa Zaben 2023 kan Sauya Fasalin Naira

Jam'iyyun SIyasa 13 a Najeriya na Barazanar Kauracewa Zaben 2023 kan Sauya Fasalin Naira

  • Jam'iyyun siyasa goma sha uku daga cikin goma sha takwas na Najeriya sun yi alkawarin kauracewa zaben 2023 da za a yi
  • Jam'iyyun sun ce ba su da bukatar fitowa zaben mataukar ba a kara wa'adin daina karbar tsofaffin kudin Najeriya
  • Sai dai jam'iyyun sun soki matakin da jihohin Kaduna, Zamfara da Kogi suka dauka na maka FG a kotu kan batun kara wa'adin

FCT, Abuja - Jam'iyyun siyasa 13 daga cikin 18 na Najeriya sun barazanar janyewa daga zaben ranakun 25 ga watan Fabrairu da na 11 ga watan Maris a Najeriya kan tsarikan Babban Bankin Najeriya kan sauya fasalin naira

A yayin jawabin da shugaban gamayyar jam'iyyun siyasan yayi a ranar Litinin, jam'iyyun 13 sun yabawa shugaba Buhari kan sauya fasalin takardun N200, N500 da N1,000, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yobe Ta Arewa: Kotun Allah Ya Isa Ta Shirya Yanke Hukunci Kan Shari’ar Lawan Da Machina

Jam'iyyun sun ce ba zasu kasance masu ra'ayin shiga zaben ba matukar ba a matsar da wa'adin 10 ga watan Fabrairun 2023 ba kamar yadda wasu gwamnonin APC suka bukata ba.

Jam'iyyun siyasan 13 sun caccaki jihohin Kaduna, Kogi da Zamfara kan yadda suka tunkari kotun koli domin samun umarnin kara wa'adin daina amfani da tsofaffin takardun nairan.

Shugaban jam'iyyar Action Alliance ta kasa, Kenneth Udeze, wanda yayi jawabi ga manema labarai, yace:

"Muna sanar da cewa, a kalla jam'iyyun siyasa 13 daga cikin 18 na Najeriya ba zasu yi zaben 2023 ba kuma akwai yuwuwar mu kauracewa dukkan lamurran zabe idan ba a gayar tsarikan sauya kudi ba ko kara wa'adin."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Online view pixel