Karancin Naira: Yadda Jihohin Arewa 3 Suka Maka Buhari Da Emefiele a Kotu

Karancin Naira: Yadda Jihohin Arewa 3 Suka Maka Buhari Da Emefiele a Kotu

  • Jihohin uku da suka hada da Kaduna, Kogi da Zamfara sun maka gwamnatin tarayya a gaban kotun koli
  • Gwamnatocin jihohin na arewa sun damu da mawuyacin halin da mutanensu ke ciki kan karancin tsabar kudi a kasar
  • Sun bukaci kotun koli ta dakatar da gwamnatin Buhari da CBN daga aiwatar da wa'adin daina amfani da tsoffin kudi

Wasu jihohin arewa uku sun juyawa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya kan manufarsa na sauya takardun naira inda suka maka shi a kotun koli.

Channels TV ta rahoto cewa jihohin na arewa da suka hada da Kaduna, Kogi da Zamfara sun nuna damuwarsu kan illar da ke tattare manufar sauya kudi na babban bankin Najeriya ya jefa mutane inda suka bukaci kotun kolin da ta dakatar da aiwatar da shi.

Kara karanta wannan

Wahala Ta Kare, Gwamnan Arewa Ya Ba Da Sabon Umarni Na Yadda Za a Saukakawa Marasa Lafiya Da Basu Da Sabbin Kudi

Buhari da gwamnonin Kogi, Zamfara da Kaduna
Karancin Naira: Yadda Jihohin Arewa 3 Suka Maka Buhari Da Emefiele a Kotu Hoto: Nasir El-Rufai, Yahaya Bello
Asali: Twitter

Jihohin arewa 3 sun maka Buhari a kotu

A cikin karar da suka shigar ta hannun lauyansu AbdulHakeem Uthman Mustapha (SAN), jihohin sun bukaci kotun da ta dakatar da gwamnatin Buhari da ta dakatar da jami'anta daga aiwatar da shirin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Saboda haka, jihohin na arewa uku suna so kotun ta hana gwamnatin tarayya aiwatar da wa'adin 10 ga watan Fabrairu a matsayin ranar da daina amfani da tsoffin N200, N500 da N1000 a matsayin kudin kasar.

Jama'a na fuskantar matsi na rashin sabbin kudi

Masu shigar da karar sun ce tun bayan sanar da manufar, ana fuskantar karancin sabbin kudi a Kaduna, Kogi da Zamfara, suna masu cewa al'ummar da suka shigar da tsoffin kudadensu a banki suna fuskantar matsin rayuwa.

Aun kuma bayyana cewa yawansu sun rasa hanyar samun sabbin kudi don gudanar da harkokinsu na yau da kullun, rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Ku Cigaba da Bin Layi Ba Zamu Kara Wa'adin Naira Ba Bayan Ranar 10 ga Febrairu, Gwamnan CBN

Masu POS sun koma siyan takardun kudi daga gidajen mai

A wani labarin kuma, mun ji cewa yayin da al'ummar Najeriya ke ci gaba da fuskantar matsin rayuwa saboda karancin kudi a kasar, masu POS sun koma dogaro da gidajen mai don gudanar da harkokinsu.

Yayin da masu POS da dama suka rufe kasuwancinsu a jihar Neja, wasu sun koma ba gidajen mai na goro domin su sayar masu da takardun kudi da suke samu daga wajen siyar da mai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng