An Kashe Mutum Shida, an Kone Kaddarori Masu Daraja Yayin Da ’Yan Bindiga Suka Kai Hari a Ondo
- Wasu tsagerun 'yan bindiga sun hallaka manoma da 'yan kasuwa a jihar Ondo, sun kwace kayayyakinsu
- Wani shugaban yankin ya bayyana yadda 'yan ta'addan ke zuwa da muggan makamai tare da farmakar mazauna
- Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce ana ci gaba da bincike don kawo mafita
Jihar Ondo - Akalla mutane shida manoma da ‘yan kasuwa aka kashe a yankunan Arimogija da Molege a karamar hukumar Ose ta jihar Ondo, Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban yankin, mr Owolafe Folorunshe ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a ranar Lahadi 5 Fabrairu, 2023, inda yace ‘yan ta’addan sun kashe ‘yan kasuwan ne da ke dawowa daga Akure, babban birnin jihar.
A cewarsa, wasu ‘yan bindiga ne a kan babura suka yi musu kwanton bauna tare da sheke su nan take tare da tattara dukkan kudaden da ke jikinsu.
Ya kara da cewa, ‘yan bindigan na yawan kai farmaki kan mutanen yankin da muggan makamai cikin dare a lokuta mabambanta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An kashe manoma
Mr. Folorunsho ya ce, a ranar Alhamis wasu 'yan ta'adda suka farmaki manoma, inda nan ma suka kashe mutane tare da lalata gonar rogo.
Ya ce:
“’Yan bindigan na ci gaba da farmakar gonaki da dare, su girbi shukanmu su ba shanunsu, A wasu lokutan, sukan zo da rana, su tursasa mu mu tone rogonmu da kanmu kuma su umarce mu mu yanka mu ba shanunsu.
“Don gujewa daukar doka a hannu, mun kai kararsu game da wannan barna ta tattalin arziki ga hukumomin da suka dace kuma sun dauki matakin fatattakarsu daga gonakin amma daga baya suka dawo suka farmake mu.”
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban yankin, Onimoru, Oba Rotimi Obamuwagun ya koka da yadda ‘yan bindigan ke barna kan mazauna yankinsa.
An lalata hekta hudu na gonar rogo
Ya yi karin haske da cewa, sun lalata sama da hekta hudu na gonar rogo ta wani da ya ci bashin banki don fara sana’ar noma, BluePrint ta ruwaito.
Da ya ziyarci yankin a karshen mako, shugaban karamar hukumar Ose, Prince Adekunlu Dennis ya bayyana damuwa game da tabarbarewar tsaro a yankin.
Ya bukaci al’ummar yankin da su hada kai da hukumonin gwamnati don tabbatar da tsaro a yankunan da ke fama da rashin tsaro.
Rundunar ‘yan sandan jihar, ta bakin jami’ar hulda da jama’a, Mrs Funmilayo Odunlami-Omisanya, ta ce jami’ai na ci gaba da bincike kan lamarin.
A makon da ya gabata ne aka kama wani matashin da ke kaiwa 'yan bindiga makamai da kayan abinci a jihar Neja.
Asali: Legit.ng