An Bada Belin Alkalai da Ma'aikatan Kotun Shari'ar Kano Da Ake Zargin Sun Sace Kudin Marayu N580m

An Bada Belin Alkalai da Ma'aikatan Kotun Shari'ar Kano Da Ake Zargin Sun Sace Kudin Marayu N580m

  • Bayan kimanin makonni biyu a gidan yari, an bada belin jami'an kotun shari'a 19 da aka garkame a Kano
  • Cikinsu akwai Alkali biyu, mai ajiyar kudi daya da kuma sauran jami'an kudi guda goma sha shida
  • Kotu ta bukaci kowanne cikinsu ya kawo mutum biyu da zasu tsaya masa amma kuma da sharruda

Kano - Kotun majistare ta bada belin Alkalan kotun shari'a biyu, da wasu ma'aikatan kotu 17 da ake tuhuma da sace kudin marayu N580.2 million a jihar Kano.

Alkalin kotun, Mustapha Sa’ad-Datti, a hukuncin da ya yanke ranar Laraba ya baiwa Alkalan biyu da wasu mutum 12 beli kan Naira milyan daya kowanne da kuma mutum biyu-biyu da zasu tsaya musu.

Alkalin ya kara da sharadin cewa wajibi ne mutum daya cikin mai tsayawa kowannensu ya ajiye kudi N200,000 a asusun kotu yayind ana biyun kuwa ya mallaka dukiya a jihar Kano mai darajar N10 million.

Kara karanta wannan

Da ɗumi-ɗumi: Daga Karshe, Kotu ta raba auren Hajiya Asiya Ganduje da Mijinta

Shari'a
An Bada Belin Alkalai da Ma'aikatan Kotun Shari'ar Kano Da Ake Zargin Sun Sace Kudin Marayu N580m
Asali: Facebook

Hussaina Imam, mai ajiyan kudi kuwa tare da wasu mutu hudu an bada belin kowanni cikinsu a kudi N10 million da masu tsaya musu biyu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sharadin shine wajibi ne daya daga cikin masu tsayawa kowanne cikinsu ya rantse cewa ba zasu gudu ba sannan kuma ya tura N5million asusun kotu.

Jaridar Vanguard ta ruwaito Alkali Sa'ad-Datti da cewa:

"Mutum na biyu mai tsayawa kowanne cikinsu kuwa wajibi ne ya mallaki dukiya da kudinta ya kai N200m a jihar Kano."

Alkali Datti ya dage zaman zuwa ranar 14 ga Febrairu, 2023.

Jerinsu: Sunayen Alkalai 2 da ma'aikatan kotun shari'a 17 da suka sace N580m

A baya mun kawo muku labarin wasu Alkalan kotun shari'a a jihar Kano tare da ma'aikatansu da suka yi amfani da matsayinsu wajen satar makudan miliyoyin marayu dake asusun bankin kotuna.

Kara karanta wannan

Fasto Ya Yada Labarin Karya Cewa Ya Mutu Gudun Kada Ya Biya Bashin N3m

Wadannan mutane su 19 sun gurfana gaban kotu ranar 19 ga Junairu, 2023.

Sunayensu sunen: Bashir Kurawa, Saadatu Umar, Tijjani Abdullahi, Maryam Jibrin-Garba, Shamsu Sani, Hussaina Imam , Sani Ali Muhammad, Sani Buba-Aliyu da Bashir Baffa.

Sauran sun hada da Garzali Wada, Hadi Tijjani Mu’azu, Alkasim Abdullahi, Yusuf Abdullahi, Mustapha Bala Ibrahim, Jafar Ahmad, Adamu Balarabe, Aminu Abdulkadir, Abdullahi Zangoda Garba Yusuf.

Asali: Legit.ng

Online view pixel