Na Rantse Ba Wanda Muke Tsoro A Kasar Nan, El-Rufa'i Ya Mayarwa Fulogan Buhari Martani

Na Rantse Ba Wanda Muke Tsoro A Kasar Nan, El-Rufa'i Ya Mayarwa Fulogan Buhari Martani

  • Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna ya yi martani ga wasu na kusa da Shugaba Muhammadu Buhari da ya ce suna yi wa Asiwaju Bola Tinubu zagon kasa
  • Gwamnan na Jihar Kaduna ya ce ba ya tsoron kowa don haka duk wani dattijo da bai girmama kansa ba za su raga masa ba
  • A bangarenta, gwamnatin tarayya ta bakin Ministan Labarai da Al'adu, Lai Mohammed ta ce bata san wadannan mutanen da El-Rufai ke nufi ba

Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya kallubalanci wasu na kusa da fadar shugaban kasa da ya yi imanin suna zagon kasa ga takarar Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a zaben 2023, Daily Trust ta rahoto.

El-Rufai ya janyo cece-kuce a ranar Laraba lokacin da ya ce akwai wasu a Aso Rock da ke zagon kasa ga takarar Tinubu.

Kara karanta wannan

Da Gaske Buhari Ya So Ahmad Lawan Ya Maye Gurbinsa? El-Rufai Ya Warware Abun da Buhari Ya Fada Masu

Gwamna El-Rufai
Ba Wanda Muke Tsoro, El-Rufa'i Ya Mayarwa Fulogan Buhari Martani. Hoto: @daily_trust
Asali: Facebook

Na rantse ba mu tsoron kowa a kasar nan, El-Rufai

Yayin da ya ke amsa tambaya a hirar da aka yi da shi a BBC Hausa, El-Rufai ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Girmama mutane ba tsoro bane, na rantse ba mu tsoron kowa a kasar nan, don haka ba tsoro muke ba, muna girmamawa amma idan ka nuna mana kai ba dattijo bane, na rantse za mu yi fada da kai."

An fitar da maganganun na gwamnan na baya-bayan nan a soshiyal midiya gabanin fitar da cikakken hirar.

El-Rufai ya yi magana ne a matsayin martani ga 'cabals' na fadar shugaban kasa a hirar da ya yi a Channels Television.

A hirar da aka yi da shi a Channels Television a shirin Sunrise Daily a ranar Laraba, El-Rufai ya ce wasu wadanda suka goyi bayan wani dan takarar a zaben fidda gwani suna boyewa bayan shugaban kasa don cimma manufofinsu.

Kara karanta wannan

Rikicin Cikin Gidan Jam’iyyar APC Yana Kara Fitowa Baro-Baro Daf da Zaben 2023

A baya El-Rufai ya ce:

"Na yi imanin akwai wasu a fadar shugaban kasa da ke son mu fadi zabe saboda ba su samu abin da suke so ba; suna da dan takararsu. Dan takararsu bai ci zaben fidda gwani ba."
"Suna son mu fadi zabe, suna boye wa bayan kokarin da shugaban kasa ke yi na aiwatar da abin da ya ke ganin shine daidai."

Martanin Gwamnatin Tarayya Ga El-Rufai

Amma, Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed ya yi martani a hukumance kan kalaman El-Rufai, ya ce gwamnati ba ta san wani a fadar shugaban kasa da ke aikata hakan ba.

Ya ce gwamnati ta kasance tana yi wa dukkan yan takara adalci ba tare da la'akari da jam'iyyarsu ba kuma Buhari ya kasance mai goyon bayan sahihin zabe na adalci.

Aisha Buhari Ta Goyi Bayan Gwamnan Kaduna El-Rufai Kan Zargin Wasu Na Yi Wa Tinubu Zagon Kasa

Kara karanta wannan

Raba gardama: El-Rufai ya fadi abin da Tinubu ya tsara yi idan ya gaji Buhari

A bangare guda, Aisha Buhari, matar Shugaba Buhari ta nuna goyon baya ga Gwamna El-Rufai kan zargin da ya yi na cewa wasu na son ganin Tinubu ya fadi zabe.

Aisha ta yi hakan ne ta hanyar wallafa bidiyon hirar da El-Rufai ya zargi wasu da yi wa Tinubun zagon kasa a shafinta na Instagram.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164