'Mutane Da Dama' Sun Makale Yayin Da Gini Ya Rufta A Abuja
- Wani babban gini mai bene hudu ya rufta a Gwarimpa a babban birnin tarayya a Abuja a ranar Alhamis, 2 ga watan Fabrairu
- Rahotanni sun nuna cewa ginin ya rufta kan mutane masu yawa duk amma ba a fayyace adadin su ba
- Hukumar bada agajin gaggawa na birnin tarayya, Abuja, FEMA, ta garzaya wurin da abin da ya faru har ta ceto mutane guda shida ta kai su asibiti
FCT, Abuja - Mutane masu yawa a halin yanzu sun makale a wani gini mai bene hudu da ya rufta a unguwar Gwarimpa na babban birnin tarayya a Abuja a safiyar ranar Alhamis, 2 ga watan Fabrairun 2022.
A halin yanzu ba a samu cikakken bayani kan lamarin ba amma majiyoyi sun ce an cire wasu gawarwaki daga ginin.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mrs Florence Wenegieme, Mukadashin darekta na hasashe, kai dauki da dakilewa, na hukumar bada agajin gaggawa na Abuja, FEMA, ta tabbatarwa jaridar Daily Trust afkuwar lamarin, tana mai cewa tawagarta sun ceto mutum shida.
Ta ce:
"An ceto mutane shida kuma an kai su babban asibitin Gwarimpa. Muna aiki domin ceto sauran mutanen."
A watan Agustan bara, wani gini mai bene biyu ya rufta a unguwar Kubuwa, wani gari da ke karamar hukumar Bwari a birnin tarayya, ya yi sanadin rasuwar mutum daya tare da wasu ma'aikata da suka makale.
Ginin, wanda ba a kammala shi ba, ya rufta ne a Hamza Abdullahi Street, off Gado Nasco Road, a Abuja.
Yara guda uku sun riga mu gidan gaskiya a yayin da ginin dakin mahaifiyarsu ya rufta a Kano
A wani labarin mai kama da wannan kun ji cewa gini ya rufta a garin Tarai da ke karamar hukumar Kibiya na jihar Kano har ya yi sanadin mutuwar kananan yara uku.
Abubakar Usman, mahaifin yaran da suka riga mu gidan gaskiya ya fada wa babban sakataren hukumar bada agajin gaggawa na jihar Kano, SEMA, Saleh Jili, hakan lokacin da ya kai ziyarar ta'aziyya a garin.
Kamar yadda jaridar The Punch ta rahoto, mahaifin ya bada sunan yaransa da suka rasu kamar haka; Aliyu Abubakar, Umar Abubakar sai kuma yar uwarsu Aisha Abubakar.
Asali: Legit.ng