Wike Ya Soke Amincewar da Ya Yi Na Ba da Filin Wasa Don Yin Taron Gangamin Atiku a Jiharsa

Wike Ya Soke Amincewar da Ya Yi Na Ba da Filin Wasa Don Yin Taron Gangamin Atiku a Jiharsa

  • Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya ce ba za a yi amfani da filin wasa a jiharsa don yin gangamin kamfen Atiku ba
  • A baya gwamnan ya ba da amincewarsa na yin amfani da filin, amma daga bisani ya sauya ra'ayi
  • Akwai 'yar tsama tsakanin gwamnan na PDP da dan takarar shugaban kasan jam'iyyar, Alhaji Atiku Abubakar da shugabanta na kasa Ayu Iyorchia

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya janye amincewar da ya yi na ba da filin taron gangamin kamfen da Atiku ya nema don yin kamfen a jihar Ribas, The Nation ta ruwaito.

Jam'iyyar PDP ta nemi a ba ta filin wasa na Adekiye Amiesimaka na jihar ta Ribas domin gudanar gangamin kamfen dan takarar shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar.

An hana Atiku filin kamfen a Ribas
Wike Ya Soke Amincewar da Ya Yi Na Ba da Filin Wasa Don Yin Taron Gangamin Atiku a Jiharsa | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: Facebook

A halin da ake ciki, gwamna Wike kuwa na kan ganiyar nuna adawa da shugabancin PDP karkashin Ayu Iyorchia saboda wasu dalilai, lamarin da ya kawo rabuwar kai a PDP.

Kara karanta wannan

2023: Wasu Masu Son Gaje Buhari Abin Dariya Ne, Gwamnan Arewa Ya Tabo 'Yan Takarar Shugaban Kasa

An tattaro cewa, soke amincewar amfani da filin wasan da a farko aka ba Atiku bisa sharadi na daya daga cikin martanin gwamnan ga nuna adawarsa da shugabancin Ayu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dalilin soke wannan amincewar ta Wike

Gwamnan ya soke amincewar da ya yi a baya ta ranar 11 ga watan Janairu a jiya Talata 31 ga watan Janairun 2023.

Ya ba da wasikar sokewan ne ta hannun kwashinansa na wasanni, Christopher Green, wanda ya tura wasikar ga gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal; daraktan kamfen na PDP a matakin kasa, Platinum Post ta tattaro.

Wasikar ta Wike ta zargi kungiyar kamfen na dan takarar shugaban kasa sashen jihar Ribas da kokarin gwama kamfen a filin tare da wani tsagi na jam'iyyar APC da Tonye Cole ke jagoranta.

Sai na tabbatar Atiku ya fadi a zaben bana, inji Wike

Kara karanta wannan

Peter Obi Zai Tashi a Tutar Babu a Jihar Arewa, Dan takarar Gwamnan Jam'iyyarsa Ya Nesanta Da Kamfen Din LP

A baya kunji yadda gwamna Wike ya bayyana aniyarsa na tabbatar da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP ya sha kasa a zaben bana.

Wike ya bayyana cewa, akwai masu yi masa bita-da-kulli a jam'iyyar PDP saboda adawarsa da shugabanta.

Ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin shugabannin PDP da gwamnonin G-5, ciki kuwa har da Wike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.