Dattijo Ya Tubure, Ya Ce Ba Zai Karbi Tiransfa Ba a Kasuwar da Zai Siyar da Buhun Wakensa
- Wani dattijo a kafar sada zumunta ya ba da dariya yayin da yace ba za a dauki buhun wakensa ba a yi masa tiransfa na kudi
- Dattijon, wanda da alamu a kasuwar hatsi yake ya ce shi dai kudi dumus kawai za a bashi, matukar ana son siyan kasyansa
- Jama’ar kafar sada zumunta sun yi martani mai daukar hankali bayan ganin bidiyon dattijon da aka yada a kafar Facebook
Wani dattijo dan Arewacin Najeriya ya turje tare da bayyana ba zai karbi kudi ta hanyar tiransfa ba, sai da a bashi a hannu.
Dattijon da ba a bayyana sunansa ba an ganshi a kasuwa yana dariya tare da nesanta bayyana ba zai siyar da buhun wakensa ba sai idan tsabar kudi za a bashi.
A bidiyon da Jaafar Jaafar ya yada a Facebook, an ji lokacin da wani mutum ke tambayar dattijon ko zai amince a tura masa kudi ta banki shi kuwa ya ba da kaya.
Cikin dariya da raha, dattijon yace sam ba zai amince ba, shi dai ya ji musu kawai kafin a dauki kayansa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Mutane da yawa a kafar sada zumunta sun yi raha da ganin wannan bidiyon, wasu sun ce basu ga laifinsa ba, domin a zamanin baya babu irin wannan tura kudi ta baki.
Kalli bidiyon:
Martanin jama’a
Ga kadan daga abin da mutane ke cewa:
Ibrahim Musa Gombe yace:
“Zaizo ya saba ai Bankin ma zuwan shi ba'a yarda dashi ba.”
Musa Muhammad Arewa yace:
“Tsoho yaji sanjin kudin buhari sau biyu kenan. 1984 chanjin kudi. 2022 chanji kudi. Baba Allah ya maka rahma.”
Ibrahim Ayuba yace:
“Jaafar Jaafar a ina ka samo bidiyon kasuwar hatsin Funtua?
“Dattawannan fa mahaifanmu ne aradu.”
Fadila H Aliyu tace:
“Tashin hankali, Baba bai yarda ya bayar da wake a ba shi lambobi ba.”
Lukman Ibrahim Barau yace:
‘Wallahi ba abun daria bane wannan. Najeriya bamu da wayewar da zamu daina amfani da kudi tsaba.”
Ibrahim G Musa Sheka yace:
“Shiyasa kuwa ai labari ya riskemu kayan abinci na ta sakkowa domin a samu kudi a hannu.”
Jikan Duduwa Funtua yace:
“Allah ya kawo Mana sauki Basu son transfer idan kana da kudi a hannu 13,000 masara”
Asali: Legit.ng