'Yan Ta'adda Sun Saka Bam a Ofishin INEC da Caji Ofis a Anambra

'Yan Ta'adda Sun Saka Bam a Ofishin INEC da Caji Ofis a Anambra

  • 'Yan bindiga sun tarwatsa ofishin 'yan sandan da na INEC a jihar Anambra ta hanyar jefa abubuwa masu fashewa gami da budewa jama'an yankin wuta
  • An ruwaito yadda hatsabiban suka kai harin da misalin karfe 2:45 na safiyar Laraba ofishin 'yan sandan na Nnobi a karamar hukumar kudancin Idemili
  • Haka zalika, yayin kai harin sun halaka wani yaro mai shekaru 16, yayin da suka harbi wata yarinya mai shekaru 15 wacce aka garzaya da ita asibiti don ceto rayuwarta

Anambra - 'Yan bindiga a safiyar Laraba sun halaka wani yaro mai shekaru 16 yayin da suka kutsa ofishin 'yan sanda da gidajen da kusa da ofishin a Nbobi a karamar hukumar Idemili da ke jihar Anambra, Daily Trust ta rahoto.

Caji Ofis
'Yan Ta'adda Sun Saka Bam a Ofishin INEC da Caji Ofis a Anambra. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Haka zalika, an ruwaito yadda 'yan bindigan suka bindige wata yarinya mai shekaru 15.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Wasu Tsageru Sun Yanka Jagoran APC Har Lahira Bayan Tinubu Ya Ci Zabe

Har ila yau, an gano yadda 'yan bindigan suka kona ofishin hukumar zabe mai zaman kanta, (INEC) a Ojoto cikin wannan karamar hukumar.

Yaron da aka halaka 'dan uwan wani 'dan sanda ne a ofishin 'yan sandan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wata majiya ta bayyana yadda 'yan bindigan suka kona hedkwatar hukumar a yankin, ta hanyar amfani fa wani abu mai fashewa (IED), jaridar Premium Times ta rahoto.

Majiyar ta labarta yadda aka garzaya da yarinyar da ta samu rauni asibiti.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Toochukwu Ikenga, ya ce harin ya faru da misalin karfe 2:45 na safiyar Laraba.

"Rundunar 'yan sandan jihar Anambra yau 1 ga watan Fabrairu ta tura jami'an tsaron jihar zuwa ofishin INEC a kudancin Idemili, Ojoto da ofishin 'yan sandan Nnobi bayan wani hari da aka yi yankin.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Wa Samanja Kisar Gilla A Cikin Gonarsa A Neja

"Hatsabiban sun zo da yawansu misalin karfe 2:45 na safiyar yau 1 ga watan Fabrairu 2023, da motoci kirar Siena guda hudu, harsasai masu linzami, da sauran abubuwa masu fashewa.
"Sun kutsa ofishin INEC, ofishin 'yan sanda da gidajen da ke cikin ofishin. Sai dai a rashin sa a, wani yaro mai shekaru 16, wanda 'dan uwan wani 'dan sanda ne a ofishin ya rasa ransa sanadiyyar bindige shi da 'yan ta'addan su ka yi, yayin da wata yarinya mai shekaru 15 ta samu matsanantancin raunin harsashi. An garzaya da ita asibiti inda ta ke samun kulawa."

- Yace.

Sai dai, kakakin hukumar INEC na jihar Anambra, Dr Kingsley Agu, bai dauki kiraye-kirayen waya ko yin martani ga sakon kar ta kwana da aka tura masa ta waya game da harin ba.

Gwamnan CBN ya isa majalisar tarayya, sun fara ganawa

A wani labari na daban, Gwamna Babban bankin Najerya, CBN, Godwin Emefiele, ya garzaya majalisar dattawan Najeriya inda aka jima ana nemansa kan tsarikan canjin takardun kudin kasar nan.

ya tsaya gaban kwamitin wucin-gadi na sauyin kudin inda yayi musu bayanan muhimman dokokin da suka shafi hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng