Dan Takarar Majalisa a NNPP Ya Saci N681m Daga Asusun Bankin Kwastomomi 400
- Ismaila Atumeyi, wani dan takarar majalisa a karkashin jam’iyyar NNPP ya saci zunzurutun kudi N500m daga asusun bankin kwastomomin bankin Union
- Dan takarar na NNPP a majalisar ya sace kudin ne ta hanyar amfani da kafar musayar kudi ta intanet inji wani shaidan da aka gabatar a kotu
- A yanzu dai Atumeyi na fuskantar tuhume-tuhume 14 da ke daga alaka da damfara a babban kotun tarayya da zama a jihar ta Legas
Jihar Legas - Dan takarar majalisar dokoki a jihar Kogi, Ismaila Yousouf Atumeyi ya shiga tasku bayan zarginsa da sace kudin da suka kai N681m daga asusun bankin kwastomomi 400 ba Union Bank.
Atumeyi, wanda mamba ne a jam’iyyar NNPP ya sace kudin ne tare da tura su asusunsa, kamar yadda shaidan da aka gabatar, Olusegun Falola ya shaidawa kotun tarayya da ke zamanta a jihar Legas.
PM News ta ruwaito cewa, shaidan, wanda jami’in bincike da kwakwaf ne na Union Bank ya ce, an gano Atumeyi ya sace kudin ne a watan Oktoban 2022 daga asusun bankin da aka saka hana cire kudi daga cikinsu.
Punch kuwa ta ruwaito cewa, Falola ya kara da cewa, Atumeyi, wanda EFCC ta gurfanar tare da Ngene Joshua Dominic da Abdulmalik Salau ana zarginsu ne da aikata mummunar dabi’ar damfara da zamba ta yanar gizo.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yadda barnar ta faru
An ce sun yi wannan barna ne ta hanyar amfani da kafar tura kudi ta Union 360 wajen cire kudaden da aka hana cirewa a wasu asusun bankin kuda 400.
A cewarsa:
“Bugu da kari, an gano cire kudaden ne ta hanyar bin diddigi ga wadanda aka turawa, Atus Homes Limited da Fav Oil and Gas Limited.
“Wadannan asusu guda biyu sun karbi kudi N681 da kuma N1.38bn bi da bi daga asusu 429 na kwastomomi.”
A cewarsa, karin bincike daga sashen bincike da kwakwaf ya nuna cewa, sa hannun Atumeyi ne a kan asusun kamfanin Atus Homes Limited yayin da na Shuaibu Yusuf da Nurudden ke kan asusun Fav Oil and Gas Limited.
A cikin makon nan ne aka kama wasu mutane da ke boye sabbin Naira tare da siyarwa mutane kan wani farashi mai tsada.
Asali: Legit.ng