Ta Karewa APC A Katsina, jigonta ya Tubure, ya fice daga Jam’iyyar, ya Nesanci Su Tinubu
- Jam'iyyar APC a jihar Katsina ta sake samun raguwa yayin da wani jigonta ya sallama ya yi ficewarsa
- Ya kuma ki karbar mukamai da aka bashi na tallata Tinubu da Dikko a jihar Katsina da kewayenta
- Jam'iyyun siyasa na ci gaba da karba da rasa mambobin gabanin zaben 2023 da ke tafe nan ba da jimawa ba
Jihar Katsina - Wani jigon jam’iyyar APC a jihar Katsina, Hon. Mamuda Lawal Musawa ya fita daga jam’iyyar da ke mulkin jihar.
Mamuda, wanda fitacce ne a fannin gine-gine kuma mai kamfanin Zamani Estate and Properties Development Ltd ya kuma ki karban nadin da tawagar kamfen din APC da aka bashi.
An ba Mamuda mukamin jakadan tawagar kamfen Jagaban/Shettima da kuma na Dikko/Jobe a zaben 2023 mai zuwa, kamar yadda jairdar Vanguard ta ruwaito.
Wannan na zuwa ne awanni 24 bayan da wasu jiga-jigan APC kuma mambobin majalisar wakilai suka bayyana ficewa daga jam’iyyar tare da marawa dan takarar PDP, Atiku Abubakar baya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Dalilin barinsa APC
A cewar Mamuda, ya fice daga APC ne saboda kakabawa ‘yan jihar dan takara tare da kin yin zaben fidda gwanin ranar 27 ga watan Mayun 2023 na ‘yan takarar majalisar tarayya ta Musawa/Matazu.
A cikin wasikar da Mamuda ya mikawa shugaban jam’iyyar APC a gundunar Musawa, ya ce ya bar jam’iyyar ne a ranar 31 ga watan Janairun 2023, Opinion Nigeria ta ruwaito.
Mamuda dai ya taba tsayawa takarar majalisar wakilai ta jiha har sau biyu amma bai yi nasara ba. Hakazalika, ya rike mukamai na siyasa da yawa a jihar Katsina da matakin kasa.
Ya kasance mamba a majalisar shura ta sake zaban shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma ta gwamna Aminu Bello Masari na jihar.
Dan Majalisar Wakilan Tarayya Daga Katsina Ya Fice Daga Jam'iyar A APC
A wani labarin kuma, kunji yadda dan majalisar wakilai na tarayya a Katsina ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar APC ta su Buhari.
Hon. Hamza Dalhat ya kuma bayyana shiga jam'iyyar adawa ta PDP domin kare muradin Atiku Abubakar.
Ana ci gaba da musayar mambobi tsakanin jam'iyyun siyasa a Najeriya yayin da zabe ke karatowa.
Asali: Legit.ng